✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsigewa: Trump ya tsallake rijiya da baya

Majalisar Dattawan Amurka ta wanke Shugaba Donald Trump a shari’ar da ake yi masa kan zargin yin amfani da mukaminsa don matsa lamba kan kasar…

Majalisar Dattawan Amurka ta wanke Shugaba Donald Trump a shari’ar da ake yi masa kan zargin yin amfani da mukaminsa don matsa lamba kan kasar Ukraine ta shafa wa abokin hamayyarsa kashin kaji.

Hakan ya kawo karshen yunkurin tsige shi daga mulki da ya raba kan Amurkawa.

Majalisar Dattawan wadda ’yan Jam’iyyar Republican ta Mista Trump  suka fi rinjaye ta kada kuri’ar wanke shi daga zargi biyu ne a jiya Alhamis.

Tuhumar farko ta yunkurin yin amfani da ofishinsa don matsa lamba kan Ukraine, ’yan majalisar 52 sun wanke shi daga tuhumar inda 48 suka nemi a tsige shi.

A daya tuhumar ta hana majalisa gudanar da aikinta, ’yan Majalisar Dattawa 53 ne suka zabi a wanke shugaban, inda 47 suka ce ya aikata laifi.

’Yan Jam’iyyar Democrat ne suka fara tuhumar Shugaban a watan Disamban bara bayan sun ce ya yi amfani da mukaminsa na Shugaban Kasa ya tursasa wa Shugaban Kasar Ukraine ya bata sunan abokin hamayyarsa na siyasa, tsohon Mataimakin Shugaban Amurka Joe Biden.

A watan Nuwamba mai zuwa Mista Trump zai kasance Shugaban Amurka na farko da aka tsige a Majalisar Wakilai da zai nemi a sake zabensa a karo na biyu.

A wani zama mai cike da tarihi da Majalisar Dattawan ta yi a shekaranjiya Laraba, ta zabi ta wanke Shugaban wanda shi ne na 45 a jerin shugabannin Amurka kan ya ci gaba da mulki.

Da an same shi da laifi da ya kasance tilas ya mika mukaminsa ga Mataimakinsa Mike Pence.

Bayan wanke Trump, ofishin yakin neman sake zabensa ya fitar da wata sanarwa cewa: “Rana ta yi halinta domin an wanke Shugaba Trump kuma yanzu lokaci ya yi na fuskantar mulkin Amurkawa.

“Sannan ’ya’yan Jam’iyyar Democrat marasa aikin yi sun san ba za su iya kayar da shi a zabe ba, shi ya sa suka so tsige shi.”