✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsinin tsingaron tsagalgalewar tsageru

Tsinin tsingaro Tsattsagar tsakin tsintar gero Tsabar maiwa da dauro Tsautsayin ga na ta tsiro Tsakuwar jifa a kwararo   Tuni an samu horo Babu…

Tsinin tsingaro

Tsattsagar tsakin tsintar gero

Tsabar maiwa da dauro

Tsautsayin ga na ta tsiro

Tsakuwar jifa a kwararo

 

Tuni an samu horo

Babu wake balle ai roro

Miyagu sun makaro

Wuyan al’umma za su shakaro

Dan agwagwa yai doro

 

Siyasa ce da tasgaro

Makirai  na ta taro

Ba su da shanu sun shiga sharo

Anai musu kidan bambaro

Haka dai lamurra suka dauro

 

Kiren karya suka kirkiro

Haurobiyawa a luro

Dan agwagwa babban toro

Tuni ya gangaro

Na-mujiya duk sun zazzaro

 

Danboto

Mai damin toto

Tuni ta zama fanko

Tana laluben na koko

Masana sun bayar da rahoto

 

Tsagalgalewar tsageru

Tsunkule-tsunkulen tsikararru

Tsabagen tsigarewar tsoro

Tsagwaron tsarin tsaro

Tsatsubar  tsunburburar  tsibirin tsuru-tsuru

 

Dabarbarun dube-duben Dabai

Kwance kullin kwabbai

Motsin mutsuttsuke matsabbai

Makircin maida kasa kuffai

Falle fama-famai a faifai

 

’Yan adawa

Na shirin dira wawa

Za su sa ai ta kuwwa

Da Baba suke kokowa

Kura za tai amai da yawa

 

Mutan Haurobiya

Kar a maishemu baya

An san masu wawushe kaya

Bayan sun yi laya

Yau sun dawo da baya

 

Tsagera

Na ta yi muku hira

Saboda toshewar basira

Yana neman a amsa masa kira

Lallai a kiyayi larura

 

An fasko dan gwanjo

Rainon Baba-Ojo

Yai karya ga su Hajjo

Zai taka rawar banjo

Ka lura Usainin-Babajo

 

Wawurar watsa wuri

Wa-ka-ci-ka-tashin wuri

Watangaririya iri-iri

Wasa da hankali kuri

Wulkita na-mujiya wuri-wuri

 

Zababbakar zabuka

Zarar zantuka

Zakalkalewar zalaka

Zumun zakuwar zuka

Zarin zagaye-zagayen bukka

 

An ce kaji sai da tsaba

Akai wa al’umma haba-haba

Ku daina yin marhaba

Da masu maishe da ’ya’ya ’yan daba

Ko ma su zam ’ya’yan dabba

 

Nai ta huduba

Kususan ga ’ya’yan Abba

Kar su yarda da sakiyar lamba

Don tana da tsananin azaba

Mugun aiki duk mu tuba

 

Mafita ake nema

Kowa sai ya kama

A tarairayi al’umma

Sai mu samu makama

Turba tagari tai ta zama

 

An dade ana ta fama

Miyagu na ta fankama

Talakawa wasu sun suma

Fatarsu  kamar an yi jima

Mu dai kara himma

 

A inganta lantarki

Samar da hasken kirki

Mu murza na’urar nikan buski

A samu na sa wa a baki

Ko a daina tsaki

 

Kar a kawo mana tarnaki

Shasshekar shakar hayaki

Bankar buki

Sunkurun shigar rukuki

Mashakon makogwaro mai makaki

 

Mai-hular saki

Ya ce yai yaki

Na ce kun ji zuki

Baba yai lakaki

Mai-duka yai mana sauki

 

’Yan miya tai zaki

Sun lashi maski-maski

Sun cika baki da mumuki

Sau tarin shurin masaki

A lura ’yan gari da baki

 

Ina kuke ’yan birni

Kui managarcin tunani

Kyawawan ta’adun iyaye da kakanni

Mu daina yi wa juna gani-gani

Cutuka ai musu magani

 

Ai ta batu na hankali

Talaka da mai hali

Ku fahimci karatun kiskali

Da faskaren kowane kauli

Ta haka ake kwance kulli

 

Tarin dukiya a baitil-mali

Ba a dauka ai fatali

Kudin gina kasa ake tattali

Aiki ne tuli-tuli

Sukuwar ingarma tai kyau da akawali

 

Ni da mutanen amana

Rani da damina

Ko an yi zafin rana

Fafutikarmu gyara ya wakana

Nunin ayyuka zai sa a bar magana

 

A nesanci masu manufar cefane

Dukiyar kasa su danne

Na-mujiyarsu su kanne

Kowace harka sun yi kane-kane

Ba su damu ba ko kasa ta kone

 

’Yan makaranta sun yi aune

An dai san zabuwa na da zane

A daina yi mana kwane-kwane

An fasko wane da wane

Masu shirin sane

 

Tsagalgalewar  tsigarewar tsageru ta ta’azzara a daukacin Haurobiya, domin Haurobiyawa ba su kyaro wadanda suka kusan cefanar da kasar nan ba, har ta kai ga bayan Babun-burin-huriyya ya kama ragamar mulki a shekara ta dubu karamin lauje da sili da babban lauje al’umma ta shiga halin ha’ula’i. Wannan duk ba wani rikirkitaccen lamari ba ne, matukar a shirye Haurobiyawa suke su fasko wadanda suka yi hada-hadar gwanjon dukiyar kasar nan.

Masana sun yi nuni da cewa kamfanonin kamfatar dukiya sama da daruruwa aka cefanar, al’amarin da ya jefa miliyoyin al’umma a zaman kashe fatari da watangaririya iri-iri a cikin gari. Yau wadanda suka tafka wannan ta’asa sun zo suna ta yi wa jama’a kuri, wai za su CETO ko su CUTAR da kasa?

’Yan makaranta mu himmatu ka’in da na’in wajen karatun kiskali, don faskaren kowane kauli, yadda za mu samu saukin kwance sasarin kowane kulli.

Batu na ingarman karfen karafunan kwangiri layin dogo, ba tare da jan kafar hannayen agogo ba, kowa yasan gyara da wuya, barna na da saukin tsuwururtawa. Matukar dai muna neman mafita, dole ne kowa ya yi kama-kama, har a samu a fice daga duma, mu yi wa nagargarun jagorori mazauni a kan darduma.