✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsofaffin Ministoci:  Akwai na ci akwai na zubarwa

A ranar Larabar makon da ya gabata ne aka rantsar da shugaba Buhari domin cigaba da mulkin kasar nan a wa’adi na biyu wanda ya sanya…

A ranar Larabar makon da ya gabata ne aka rantsar da shugaba Buhari domin cigaba da mulkin kasar nan a wa’adi na biyu wanda ya sanya yanzu aka zura ido ana jiran ganin irin mutanen da shugaban zai nada domin su taimaka masa wajen gudanar da harkokin mulkinsa.

Tun kafin shugaba Buhari ya kammala wa’adinsa na farko ake ta hura masa wuta ya canja shugabannin rundunonin tsaron kasar nan saboda ana ganin sun gaza wajen tabbatar da tsaro a kasar nan, musamman a yankunan Arewa maso gabas da wadansu yankuna na Arewa maso yamma, amma shugaba Buhari ya ki canja su, inda a karshen watan jiya a wata hira ta musamman da aka yi da shi a gidan talabijin na kasa (NTA) ya bayyana cewa bai canja su ba ne saboda shi tsohon soja ne ya san illar canja kwamanda a lokacin da yaki ya yi tsanani.

Haka nan kuma an yi ta hura masa wuta domin ya canja ministocinsa, a nan ma ya kawar da kai daga kiraye-kirayen da ake yi masa, inda ya bar duk ministan da ya nada tun farkon mulkinsa har sai da ya kai karshen wa’adin mulkinsa na farko, sai wanda ya rasu ko wadanda suka ajiye aikin da kansu.

Alal hakika duk da an yi ta kokawa game da ministoci da wadansu manyan jami’an gwamnatin tarayya da shugaba Buhari ya nada da aka bukaci ya canja wadansu daga cikinsu amma ya ki yarda har da suka kai karshen wa’adin mulkinsa, duk da haka akwai wadansu daga cikinsu da suka yi kokari sosai da ya kamata a sake nada su domin su cigaba da kyawawan ayyukan da suka faro.

Sai dai kuma akwai wadansu daga cikinsu da sun gaji sosai saboda yawan shekarunsu, yanzu an wuce zamaninsu, yanzu zamani ne na kwamfuta, sai a yi abubuwa da dama ba su gane ba, kuma duk tunaninsu irin na da ne wadanda ba su yi daidai da zamanin da ake ciki ba, saboda haka ya kamata a canja su a kawo wadanda suka yi daidai da zamani.

Ya kamata a fahimci cewa yawan canja shugabanni ba alheri ba ne, domin yadda ake nade-nade a kasar nan ya nuna ba ana yi ne domin a yi aiki ba, ana yi ne domin wanda aka nada ya samu na cefane kawai. Domin babu yadda za a yi komin basirar mutum da zuwansa ma’aikatar da aka tura shi ya fara gudanar da wani aiki, dole sai ya zauna ya yi nazarin abubuwan da ke faruwa a ma’aikatar. Kuma akalla sai ya kwashe watanni shida ko shekara guda kafin ya gano bakin zaren. Amma a daidai lokacin da ya gano bakin zaren kuma sai a cire shi a kawo wani. Ta yaya za a cigaba ta wannan tsarin?

Haka kuma sai a rika tura mutum ma’aikatar da ba shi da kwarewa a harkokinta, inda za a tura lauya ma’aikatar lafiya ko a tura akanta ma’aikatar ilimi a matsayin minista. Kamata ya yi a tura mutane ma’aikatun da suka kware domin su yi aiki da kwarewarsu, watau a tura lauya ma’aikatar shari’a, masanin noma  a tura shi ma’aikatar noma, masanin kudi kuma ma’aikatar kudi, masanin lafiya ya tafi ma’aikatar lafiya, da sauransu.

A shekarun baya a zamanin mulkin Janar Sani Abacha na tattauna da marigayi tsohon gwamnan jihar Kano Alhaji Abubakar Rimi, lokacin da yake rike da mukamin ministan sadarwa, inda ya nuna takaicinsa game da yadda ake yawan canja ministoci ba tare da an ba su damar yin aikin da aka nada su ba.

Ya ce akwai lokacin da suka tafi wani taro na ministocin sadarwa na kasashen nahiyar Afirka sai ya hadu da ministan sadarwa na kasar Misira na wancan lokacin,  inda ya tambayi Rimi yanzu kai ne ministan sadarwa na Najeriya? Rimi ya ce  masa kwarai kuwa, sai ministan Misiran ya rika tambayar sa tsofaffin ministocin sadarwa na Najeriya da ya yi zamani da su a baya, yana ce masa ina su wane da wane? Ministan na Misira sai ya fada wa Rimi cewa shi yana rike da mukamin ministan sadarwa na Misira tun shekarar 1976.

Alhaji Abubakar Rimi ya ce da ya ji haka sai ya kidaya ministocin da aka yi a ma’aikatar sadarwa ta Najeriya daga shekarar 1976 zuwa 1994, sai ya ga cewa shi ne minista na goma sha biyu a ma’aikatar sadarwar. Ya ce, ta yaya za a yi aiki alhali ana nada mutum mukami kafin ma ya kammala nazari failoli an cire shi?  Ya ce wannan ministan na Misira babu abu da bai sani ba a ma’aikatarsa saboda dade wa da ya yi a wurin.

Saboda haka kamata ya yi duk wanda aka nada a kan wani mukami to lallai ne a ba shi isasshen lokacin da zai yi aiki. Da dama daga cikin ministocin da suka sauka yanzu sun riga sun fahimci ma’aikatun da suka bari, amma ga shi sun bar ma’aikatun. Saboda haka a zakulo masu himma daga cikinsu a mayar da su ma’aikatunsu domin su ci gaba da ayyukan da suka fara, maimakon a nada sabbi da sai sun dauki lokaci kafin su gane inda aka sanya gaba.

Ya kamata a guji nada mutane a mukami domin a saka masu saboda kokarin da suka yi a fagen siyasa, ba domin cancantarsu ba. Idan aka yi haka an mayar da dukiyar gwamnati ganima ke nan ba amana ba.

Haka kuma ya kamata a wannan zubin a raba ma’aikatar wutar lantarki da ayyuka da gidaje kashi uku, yadda za a samu ministoci guda uku, ta haka za a rage wa ministan wannan ma’aikata aiki, domin an tara masa ayyuka da yawa

Amma raba ma’aikatar zai kara samar da ayyukan yi ga ‘yan Najeriya saboda ministocin guda za su dauki masu taimaka masu da sauransu.

Allah Ya bayar da ikon nada shugabanni masu kishin jama’a ba masu bukatar wawushe dukiyarsu ba.