✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsofaffin ’yan kwallon Super Eagles sun nemi Gwamnatin Tarayya ta cika alkawarin gidajen da ta yi musu

Tsofaffin ’yan kwallon Super Eagles da suka lashe kofin Afirka a shekarar 1994 a Tunisiya sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta yi wa…

Austin EguavoenTsofaffin ’yan kwallon Super Eagles da suka lashe kofin Afirka a shekarar 1994 a Tunisiya sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta yi wa Allah ta cika musu alkwarin gidajen da ta yi musu a wancan lokaci.
Sun nuna bukatar haka ne a lokacin da Kyaftin din kungiyar a wancan lokaci Austin Eguaboen ya wakilci wasu daga cikin tsofaffin ’yan kwallon a ziyarar da suka kai wa Ministan Wasanni Malam Bolaji Abdullahi a ranar Litinin da ta wuce a ofishinsa da ke Abuja.
A lokacin da kungiyar kwallon kafa ta kasa watau Super Eagles ta lashe kofin Afirka a karo na biyu a Tunisiya a shekarar 1994 gwamnati mai ci a wancan lokaci ta Marigayi Janar Sani Abacha ta yi musu alkwarin ba kowane daga cikin ’yan kwallon gida amma har yanzu ba a cika musu alkawarin ba.
Eguaboen sun kai ziyarar ga Ministan ne tare da Samson Siasia da bictor Ikpeba da kuma Ben Iroha a madadin daukacin tsofaffin ’yan kwallon.   Sun nuna takaicin ganin yau kimanin shekara 19 kenan da wancan alkawari amma har yau gwamnati ta kasa cika wa.
A nasa jawabin, Ministan Wasanni Malam Bolaji Abdullahi ya yi alkwarin gabatar da bukatarsu ga shugaban kasa Goodluck Jonathan don ganin gwamnati ta yi wani abu a kai.  
Ya jinjina musu a kan irin hakurin da suka nuna na tsawon lokaci da kuma yadda wasu daga cikinsu suka mutu ba tare da gwamnati ta cika alkawarin da ta yi musu ba.
“Ko shakka babu kun daukaka martabar kasar nan a idon duniya na lashe kofin Afirka a shekarar 1994 don haka gwmanati za ta yi duk mai yiwuwa don ganin an cika alkarin da ta yi muku a wancan lokaci”, inji Minista Bolaji.
Daga cikin ’yan kwallon da suka rasu da ke cikin tsofaffin kungiyar akwai Rashidi Yekini da Thompson Oliha.