Search
Subscribe
Tsohon Babban Jojin Jihar Kebbi ya zama Magajin Malam na Gwandu

Tsohon Babban Jojin Jihar Kebbi ya zama Magajin Malam na Gwandu

Mai martaba Sarkin Gwandu Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar ya nada tsohon Babban Jojin Jihar Kebbi, Alhaji Ibrahim Umar, a matsayin Magajin Malam  din Gwandu. An nada Alhaji Ibrahim Umar ne a ranar Larabar makon jiya inda ya gaji mahaifinsa Malam Umaru Na- hayyu, (Magajin Bunga) kuma an gudanar da nadin ne a fadar Abdullahin Gwandu da ke Birnin Kebbi.

Da yake jawabi Mai martaba Sarkin Gwandu Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar ya ce dalilin da ya sa masaurautar ta nada shi Magajin Malam din Gwandu, shi ne tsohon Babban Jojin ba karamar gudunmawa yake bayarwa ba tun ana tsohuwar Jihar Sakkwato har aka dawo Jihar Kebbi. Kuma mahaifinsa Malam Umaru Na-hayyu shi ne Magajin Bunga har lokacin da Allah Ya yi masa rasuwa.

Sarkin ya yi kira ga sabon Magajin Malam din Gwandu ya ci gaba da bayar da irin wannan gudunmawar da yake ba jihohin Kebbi da Sakkwato da kuma Najeriya baki daya domin irinsu ake so a kasa saboda sanin dokoki da kuma ba mai hakki hakkinsa. Ya ce duk mutumin da ya kai matsayin Babban Joji har ya yi ritaya dole ne kasarsa ta karu da shi domin zai rika ba da gagarumar gudunmawa a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Da yake jawabin godiya, Alhaji Ibrahim Umar, cewa ya yi ’’Ina godiya ga Allah Wanda cikin ikonSa a yau aka nada ni wannan sarautar ta Magajin Malam Gwandu, wadda Masarautar Gwandu ta tabbatar min da ita tun shekara hudu da suka gabata, yau Allah Ya nuna mana ranar wannan nadi.”

Magajin Malam Gwandu ya kara da mika godiya ta musamman ga Mai martaba Sarkin Gwandu Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar da ’yan Majalisar Sarkin Gwandu da daukacin ’yan uwa da abokan arziki. Kuma ya yi ban- gajiya ga wadanda suka halarci taron nadin tare da fatan Allah Ya saka wa kowa da alherinsa.

An haifi Magajin Malam Gwandu, a garin Birnin Kebbi a ranar 7/10/1947, kuma ya yi karatun firamare a makarantar ’Yar-Yara, Birnin Kebbi daga nan ya wuce zuwa makarantar Midil ta Birnin Kebbi ya kuma je Kwalejin Nagari da ke Birnin Kebbi daga nan sai Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya daga 1967-1969 inda ya samu Diploma a fannin shari’a daga nan ya yi  Digiri a fannin shari’a daga 1971-1974. Ya  halarci Makarantar Horar da Lauyoyi da ke Legas daga 1974-1975 daga nan sai ya wuce aikin hidimar kasa (NYSC) a garin Ibadan.

Ibrahim Umar ya yi ayyukan gwamnati da suka hada da malamin gona mai daraja ta biyu ya kuma yi rijistara a kotu, ya kuma yi sufeton kotuna na shiyya ya zama Majistare mai daraja ta biyu a Gusau ya kuma taba zama Babban Majistare, sannan ya rike Babban Rajistara na Babbar Kotun tsohuwar Jihar Sakkwato a 1982.

An nada shi Sakataren Hukumar Sake Fasalin Dokoki (Law Reform Commission), kuma ya zama Babban Sakatare a Ma’aikatar Shari’a daga sannan ya zama Kwamishinan Shari’a na tsohuwar Jihar Sakkwato daga 1983-1986 daga nan ya zama alkali a Babbar Kotun Jihar Sakkwato daga 1986-1988, sai kuma ya zama Babban Jojin tsohuwar Jihar Sakkwato.

Bayan kirkiro Jihar Kebbi ne sai ya dawo gida ya ci gaba da rike mukamin Babban Jojin Jihar, inda ya yi ritaya a kan wannan matsayin da ya fi kowa dadewa bisa wannan mukami a Najeriya domin ya fara wannan matsayi ne tun 1988 zuwa shekarar 2012 daga tsohuwar Jihar Sakkwato zuwa Jihar Kebbi.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin