Da Dumi Dumi

Tsohon dan kwallon Brazil ya musulunta

Rahotanni da ke fiowa daga Saudiyya sun nuna tsohon dan kwallon Brazil Sergio Ricardo wanda aka fi sani da Nebes ya Musulunta a Larabar makon jiya a kasar Saudiyya.

Sergio wanda ya shafe shekaru da dama yana kwallo a kulob da dama a yankin Gabas ta Tsakiya ya yi wa kulob da dama wasanni a Turkiyya da Katar da kuma Saudi Arabiyya.

Abokinsa na kut-da-kut da suka yi wasa tare a kulob din Al-Ittihad na kasar Saudiyya Mohammed Suwaid ne ya sanar da Musuluntar Ricardo a shafin sadarwarsa na Twitter.

“Alhamdulillah, yanzu na zama Musulmi kuma wannan ita ce shawara mafi girma da muhimmanci da na yanke a rayuwata” inji Ricardo a wani faifan bidiyo da abokinsa Mohammed suwaid ya baza a shafinsa na twitter jim kadan da Musuluntarsa.

Sergio Ricardo dai ana masa lakabi ne da Nebes a Gabas ta Tsakiya a lokacin da yake kwallon kafa.  Ya shafe shekara 4 yana buga wa kulob din Al-Ittihad da ke Jeddah kulob din da ya fi kowane kulob tsufa a Saudiyya.

ADVERTISEMENT

Kafin nan ya taba buga wa kulob din Al-Ahli da ke Jedda da kuma na Al-Hilal da ke birnin Riyad na Saudiyya.

Bayan ya bar Saudiyya a 2005 sai ya koma wani kulob a Katar mai suna Al-Gharafa kafin ya sake komawa wani kulob a Saudiyya mai suna Alread da ke birnin Buraidah.

Ya yi ritaya daga yin wasan kwallon kafa ne a 2010 bayan ya yi wasa a kulob din Botafego da ke birnin Rio de Janaeiro da ke Brazil.

Tun daga wancan lokaci bai sake zuwa Saudiyya ba sai a ranar Larabar makon jiya inda ya kai wa abokansa ziyara kuma a ranar ce ya karbi addinin Musulunci kamar yadda abokinsa Suwaid ya sanar da duniya halin da ake ciki.

Jim kadan bayan Suwaid ya watsa labarin Musuluntar Ricardo a shafinsa na twitter sai dubban mutane suka rika rububin aika sakonnin murna da na fatan alheri ga Sergio Ricardo.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya