✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon dan kwallon Turkiyya ya zama dan tasi

Tsohon dan kwallon Inter Milan da ke Italiya da Galatassarary da ke Turkiyya da kuma Blackburn Robers da ke Ingila Hakan Sukur ya koma tukin…

Tsohon dan kwallon Inter Milan da ke Italiya da Galatassarary da ke Turkiyya da kuma Blackburn Robers da ke Ingila Hakan Sukur ya koma tukin tasi a Amurka don samun na abinci bayan rayuwa ta yi masa kunci.

Sukur ne da kansa ya bayyana haka ga manema labarai a ranar Litinin da ta gabata a Amurka inda yanzu yake zaune don ci gaba da rayuwa.

Sukur, wanda ya taimaki Turkiyya wajen kaiwa mataki na uku a gasar cin Kofin Duniya da aka yi a shekarar 2002 a Koriya da Japan ya ce rayuwa ta juya masa baya bayan da ya samu sabani da Shugaban Kasar Turkiyya Recep Erdogan a 2011 lokacin da ya shiga harkokin siyasa bayan ya yi ritaya daga kwallon kafa kuma aka zabe shi dan majalisa a Turkiyya.

Shugaba Erdogan ya sa kafar wando daya da mutane da dama a gwamnatinsa wadanda ya yi zargin suna da hannu a yunkurin yi masa juyin mulki, kuma Sukur yana daya daga cikinsu.

Sukur ya ce “Rayuwa ta yi mini kunci a Turkiyya inda na rika samun barazanar kisa, an garkame mahaifina a gidan yari, an tsangwami matata da ’ya’yana wanda hakan ya sa na bar kasar zuwa Amurka ba tare da shiri ba.”

“Bayan na koma Amurka ce sai na bude shagon buga litattafai amma ganin yadda batagari suke yawan kai mini hari ya sa na koma tukin tasi,” inji shi.

Sukur ya ce Shugaba Erdogan ya kwace daukacin dukiyarsa kuma hakan ya sa ya talauce.

Sukur mai shekara 48 yana daga cikin ’yan kwallon Galatassaray na Turkiyya da suka doke kulob din Arsenal a wasan karshe na gasar cin Kofin UEFA da yanzu ake kira Europa a shekarar 2000. Sannan ya kafa tarihi a gasar cin Kofin Duniya a 2002 bayan ya zura kwallo mafi sauri a sakan 10.8 da fara wasa a ragar Koriya ta Kudu inda Turkiyya ta zama ta uku a gasar.