✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon Gwamnan Kebbi ya gargadi matasa kan bangar siyasa

Tsohon Gwamnan farar hula na farko a Jihar Kebbi, Alhaji Abubakar Musa Garkuwan Yauri ya shawarci matasan kasar nan da kada su bari a yi…

Tsohon Gwamnan farar hula na farko a Jihar Kebbi, Alhaji Abubakar Musa Garkuwan Yauri ya shawarci matasan kasar nan da kada su bari a yi amfani da su wajen bangar siyasa a zabe mai zuwa, musamman matasan Jihar Kebbi.
Alhaji Abubakar Musa ya kuma gargade su kan shan miyagun kwayoyi wanda ya ce ba ya da wani amfani a gare su.
Tsohon Gwamnan ya yi kiran nan ne a lokacin da ya je Kaduna domin kaddamar da ’yan kwamitin amintattu na kungiyar Al’ummar Jihar Kebbi mazauna Kaduna.
Garkuwan na Yauri ya kuma tunatar da iyaye kan nauyin da Allah Ya dora a kansu na tarbiyyantar da ’ya’yansu.
Ya ce kamata ya yi iyaye su tabbatar sun tashi tsaye matuka wajen ganin ba a yi amfani da ’ya’yansu wajen bangar siyasa ko ta da rikici ba.
“ Ina kira ga matasa su kaurace wa bangar siyasa domin ba ya da wani amfani. Kuma ina ba su shawara su guje wa mu’amala da kwayoyi saboda idan matasa suna mu’amala da kwayoyi dole a rika samun karuwar aikata miyagun laifuffuka.
Muna so matasa su sani cewa su ne manyan gobe don haka dole ne mu tabbatar sun zama mutanen kirki saboda su mulki jiharmu da kasa baki daya cikin nasara. Babu iyayen da ke son ganin ’ya’yansu sun lalace a cikin al’umma,” inji shi.
Tsohon Gwamnan ya kuma yi kira ga shugabbani da iyayen kungiyar su ji tsoron Allah su tafiyar da kungiyar yadda ya kamata domin amfanin ’yan asalin Jihar Kebbi da ke Kaduna.
Ya nemi su hada kai a duk inda suka samu kansu, ya ce idan babu hadin kai babu yadda za a yi a samu biyan bukata ko cimma manufofin kungiyar.
Da yake jawabi a wurin, shugaban kungiyar Injiniya Abubakar Sadik dakingari cewa ya yi sun kafa kungiyar ce shekara biyar da suka wuce domin taimaka wa ’yan Jihar kebbi mazauna Kaduna.
Ya ce daga cikin abubuwan da suka tsara sun hada da biya wa yaran Jihar Kebbi kudin jarrabawa na WAEC da NECO da kuma NDA.
Sai taimaka wa mambobinta ’yan kasuwa domin bunkasa kasuwancinsu da samar da cibiyoyin koyar da sana’o’i da sauransu.
A jawabinsa a madadin ’yan Kwamitin Amintattu, Ambasada Umar Faruk Ka”oji ya nanata muhimmancin hadin kai a tsakanin al’ummar Jihar Kebbi inda ya sha alwashin za su yi iya kokarin yin adalci wajen sauke nauyin da aka dora musu.