✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon Kwamishinan Lafiya na Kaduna Dakta Tukur ya rasu

Tsohon Kwamishinan Lafiya na jihar Kaduna Dakta Abdullahi Muhammad Tukur, ya rasu. Ya rasu ne a babban asibitin kasa da ke Abuja a jiya Laraba…

Tsohon Kwamishinan Lafiya na jihar Kaduna Dakta Abdullahi Muhammad Tukur, ya rasu. Ya rasu ne a babban asibitin kasa da ke Abuja a jiya Laraba da daddare, a yau Alhamis za a yi jana’izarsa inda za a yi masa sallah a masallacin Sultan Bello Kaduna sannan a birne shi a makabartar Unguwan Sarki Muslim.

Dakta Abdullahi, ya yi aiki a ma’aikatar lafiya daga shekarar 1972 zuwa 1975, sannan ya zama Kwamishinan Lafiya daga 1976 zuwa 1978. Ya kuma rike mukamin shugaban Hukumar lafiya ta jihar Kaduna daga 1980 zuwa 1983. Daga bisani ya ritaya sannan ya bude asibiti mai zaman kanshi mai suna, Jinya Hospital, Kaduna.

Cikakken rahoton na nan tafe.