✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon Minista ya lashe zaben gwamnan Bauchi

Tsohon Ministan Abuja, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya zama sabon Gwamnan jihar Bauchi a jam’iyyar adawa ta PDP. Bala Muhammad ya doke gwamna mai ci…

Tsohon Ministan Abuja, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya zama sabon Gwamnan jihar Bauchi a jam’iyyar adawa ta PDP.

Bala Muhammad ya doke gwamna mai ci ne Muhammed Abdullahi Abubakar dan takarar jam’iyyar APC.

PDP ta lashe zaben ne da kuri’a 515,113, yayin da APC da ke mulki a jihar ta samu kuri’a 500,225.

Baturen zaben jihar Farfesa Mohammed Kyari, ne ya sanar da sakamakon inda y ace, Sanata Bala ne yake da mafi rinjayen kuri`u a zaben `yan takarar Gwamnan jihar da aka yi.