Search
Subscribe
Tsohon shugaban Faransa Jacques ya mutu

Jacques Chirac

Tsohon shugaban Faransa Jacques ya mutu

Tsohon shugaban Faransa Jacques Chirac, wanda ya yi fama da zarge-zargen cin hanci da rashawa bayan ya sauka daga mulki, ya mutu yana da shekara 86.

Surukinsa ya shaida wa kamfanin dillancin labaria na AFP cewa “Shugaba Jacques Chirac ya mutu a safiyar yau Alhamis cikin kwanciyar hankali zagaye da iyalansa.”

Jacques, ya yi shugabancin Faransa sau biyu kuma shi ne shugaban da ya shugar da kasarsa cikin kungiyar kasashen turai da ke amfani da kudi bai-daya.

Rahoton BBC.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin