✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon Shugaban Kasar Masar Hosni Mubarak ya rasu yana da shekara 91

Hosni Mubarak, wanda ya shugabanci kasar Masar na kimanin shekara 30, ya kuma sauka bayan juyin juya halin shekarar 2011, ya rasu, yana da shekara…

Hosni Mubarak, wanda ya shugabanci kasar Masar na kimanin shekara 30, ya kuma sauka bayan juyin juya halin shekarar 2011, ya rasu, yana da shekara 91.

Gidan telebijin na kasar ya bayar da rahoton rasuwarsa, a yau Talata, makonni bayan an masa aikin tiyata.

Mubarak dai shi ne ya kasance Shugaban Kasar Masar na hudu, inda ya fara mulkar kasar tun shekarar 1981 har zuwa lokacin da aka hambarar da shi a wata zanga-zangar bijirewa da aka yi wa lakabi da Zamanin Juyin Juya Halin Kasashen Larabawa.

Bayan ya yi fama da doguwar jinya, tsohon shugaban ya rasu bayan ya jagoranci kasar daga shekarar 1981 zuwa 2011.