✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon Shugaban PDP na Jihar Kebbi ya koma APC

Wani na hannun damar tsohon Gwamnan Jihar Kebbi Alhaji Adamu Aliero kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Alhaji Sani Hukuma Zauro, Zannan Gwandu ya…

Wani na hannun damar tsohon Gwamnan Jihar Kebbi Alhaji Adamu Aliero kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Alhaji Sani Hukuma Zauro, Zannan Gwandu ya canja sheka daga jam’iyyar zuwa Jam’iyyar APC.
Alhaji Sani Zauro wanda ya shaida wa manema labarai haka a Birnin Kebbi, ya ce ya yi haka ne saboda ya ga har yanzu Gwamna Sa’idu dakingari bai dauke su cikakkun ’ya’yan PDP ba.
Zannan Gwandun ya ce tun lokacin da suke Jam’iyyar CPC inda aka nemi su dawo PDP tare da yi musu wasu alkawuran ba wasu daga cikin mutanen Sanata Adamu Aliero mukamai a gwamnatinsa har yanzu ba a cika ba.
Alkawuran dai sun hada da ba magoya bayan Sanata Aliero mukaman mashawarta 10 da kwamishinoni da shugabannin kananan hukumomi da ba su katin zama ’yan Jam’iyyar PDP, “Kuma duk da zunzurutun kudi har Naira milliyan 20 da Sanata Aliero ya bayar amma ba a yi musu rajistar ba,” inji shi.
Ya ci gaba da cewa ganin wulakancin da ake yi ga ubangidansu Sanata Adamu Aliero na daga cikin dalilansa na ficewa daga Jam’iyyar PDP zuwa APC inda suke ganin za a iya yi musu adalci tare da tsayar da ’yan takarar da jama’a ke so.
Alhaji Zauro ya yi kira ga ’ya’yan Jam’iyyar APC su hada kai da bangarensu da suka shigo domin ganin jam’iyyar ta lashe zabe mai zuwa idan Allah Ya kai badi.