Search
Subscribe
Tsokaci ga Shugaba Muhammadu Buhari II

Tsokaci ga Shugaba Muhammadu Buhari II

Yakan zama dole koyaushe a yi tsokaci ga shugabannin duniya domin sun hau mulki ne da yardar talakawa da suka zabe su maimakon zuwa kai-tsaye ta mulkin soji. Gaskiya mu dai a Najeriya mun shiga taskun rayuwa ba don komai ba kuwa sai don mun hadu da shugabannin da ba sa sauraren koke-koken talakawansu sai kawai masu yi musu fadanci a cikin rediyo ko masu rubuce-rubuce ko kuma wadansu ’yan siyasa wadanda ke kasancewa su ne suke sharbar romon dimokuradiyya.

Wannan ya kunno kai tun daga kananan hukumomi zuwa jihohi sannan ya bulla har Gwamnatin Tarayya. Gaskiya, ya zama dole a fito fili a sanar da Shugaba Buhari cewa hanyoyin mulkin wannan kasa duk an rufe wa talakawa kuma ana cikin rudani domin kuwa koda wadansu na cewa ba a yunwa wai sai dai a ce ana matsi, wato rayuwa ta shiga babbar matsala, duk  inda aka samu babbar matsala to yunwa ita ce sanadi. Kuma su wadancan da ke cewa babu yunwa a cikin kasa mutane ne wadanda ba su san babu ba tun lokacin kuruciyarsu har yanzu da suka kai shekarun karshe. Kowane daga cikinsu ya yi nesa da talakawa domin sun gina manyan gidaje da masana’antu jingim ga kuma gidajen gona masu yawan gaske ga shanu irin na kasashen waje, saboda haka yaya mai dukiya irin wannan zai san halin da talaka yake ciki?

Shugaba Buhari shi ma yana da gidan gona, amma bai ce talakawa ba sa cikin jidalin yunwa ba, sai wani dan-kidanka-na jiyo kawai don ya samu mukamin da yake jira a ba shi domin kece-raini ga abokan gabarsa wato talakawan Najeriya.

Gaskiya Shugaba Buhari kai ne ka ce a shekarar 2015, an ba ka mutanen da ba ka sansu ba, saboda haka a 2019 kai ne da kanka za ka zabo mutanen da suka dace domin kyautata wa Najeriya. Koda yake idan za a duba sosai kuma a yi bincike, lokacin Obasanjo yakan ba wa gwamnonin jam’iyyarsa damar kawo mutane dai-daya domin zama ministoci wanda kai Shugaba Buhari ka ce ba ya cikin ka’idar tsarin mulki. Wannan dalili ne ya sa wadansu ’yan siyasa da ake kira ‘mu ne na bara mu ne na bana’ suka fice daga APC suka koma gidansu na tsamiya wato PDP.

Gaskiya Shugaba Buhari yanzu ka nemo naka mutanen, amma wadansu sun ce wai an yi kitso da kwarkwata, domin za a ga watakila bara ta fi bana yabanya. Shugaba Buhari wallahi mun zabe ka tun lokacin da ka shigo siyasa wato 2003, ko da yake tun 1999 ake so ka shigo siyasar domin farin jinin da kake da shi wurin talakawan Najeriya. Amma ka ce kai ba ka son shiga siyasa, saboda ’yan siyasa barayi ne, to wane tudu wane gangare sai ga shi yau Allah Ya ba ka kujerar da ta fi kowace kujera a Afirka kuma ka yi shekara hudu na farko kuma ga wanda kuke cewa “Nes-Lebul” a ta bakin maigidana Farfesa Ibrahim Malumfashi!

To ya shugaba Buhari! Na san cewa shugabancin kasa kamar Najeriya wallahi sai jurarre kuma mai hakuri ainun, domin ilimin zamani ya sa babu kishin kasa a rayukan ’yan boko, abin da za su samu shi ne komai gare su. Wannan mummunar bukata ita ce ummul-haba’isin jagulewar komai a Najeriya.

Gaskiya ne sojojin da suka yi mulki sun yi gyara kuma sun bata zamantakewar al’ummar kasa wajen rarraba kawunanmu, domin su samu damar mulkar mutane cikin razani.

To yanzu dai dole Shugaba Buhari ya fahimci rikice-rikicen da suka addabi wannan kasa ba ma kamar Arewacin Najeriya inda lamarin ya fi muni kwarai da gaske. Ba a ce Shugaba Buhari ya nuna son kai ba, amma gaskiya muna bukatar agaji koda yake ya ce mu ’yan wannan gefen ci-ma-zaune ne koda kuwa abin haka yake me ya jawo hakan?

Rage kudaden tafiye-tafiyen ministoci ba shi ba ne kawai ke da ma’ana har da rage albashin ’yan majalisa sama da kasa da rage kudaden da ake kashewa a fadar gwamnatinka yana da muhimmanci. Tafiye-tafiye na dukkan jami’an gwamnati ba dole ba ne, ganin Ingila, Faransa, Amurka da sauran kasashen Turai, ba sa yin irin wadannan tafiye-tafiye barkatai. Kuma yadda suke biyan albashinsu da na ’yan majalisarsu sun sha bamban da namu. Lallai ne a ga cewa in talakan kasa yana cikin wahala shi ma Shugaba a gan shi ciki.

Kwamared Ibrahim Abdu Zango, Kano. (08175472298)   

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin