Da Dumi Dumi

Tsoron Kurona: Iran za ta saki fursinoni dubu 54

Nazanin Zaghari-Ratcliffe, jami’ar agaji da ake sa ran sakinta daga kurkukun Iran
Nazanin Zaghari-Ratcliffe, jami’ar agaji da ake sa ran sakinta daga kurkukun Iran

Kasar Iran za ta saki dubban fursunoni na wani dan lokaci a yayin da kasar take kokarin takaita yaduwar cutar Kurona, kamar yadda mahukunta suka bayyana.

Fiye da fursinoni dubu 54 ne za a saki bayan da aka yi musu gwajin da ya tabbatar da cewa ba sa dauke da cutar, a cewar mai magana da yawun Ma’aikatar Shari’a ta Kasar, Gholamhossein Esmaili.

Sai dai ya ce ba za a saki fursunonin da ke barazana ga tsaron kasar ba, wadanda aka yanke wa daurin fiye da shekara biyar a gidan kaso.

Ma’aikaciyar agajin nan ’yar Birtaniya ’yar asalin Iran, Nazanin Zaghari-Ratcliffe da ke tsare a kurkuku watakila a sako ta, kamar yadda Majalisar Dokokin Birtaniyar ta nuna.

Mijinta Tulip Siddik, ya ruwaito Jakadan Iran a Birtaniya yana cewa “Watakila a sako Misis Zaghari-Ratcliffe daga gidan kaso yau ko gobe.”

ADVERTISEMENT

Mijinta ya fadi a karshen mako cewa ya yi amanna mai dakinsa ta kamu da cutar Kurona; sai dai jami’an gidan yarin sun ki su yi mata gwajin cutar.

Kimanin mutum 77 ne suka rasa rayukansu a Iran sakamakon cutar Kurona, wadda ita ce kasar da aka fi mutuwa sanadiyar cutar bayan kasar China, kuma mutum 2,336 ne suka kamu da cutar a Iran.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya