✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsuntsu ya kashe mai shi a Amurka

Wani babban tsutsu da ake kira cassowary, da yake da dogayen faratu a kafafunsa ya kashe mutumin da ya mallake shi a gidan da ake…

Wani babban tsutsu da ake kira cassowary, da yake da dogayen faratu a kafafunsa ya kashe mutumin da ya mallake shi a gidan da ake kiwonsa a garin Gainesbille da ke Jihar Florida a Amurka. Kamar yadda kafar labari ta CNN ta ruwaito.

Wanda ya mallakin tsuntsun cassowary mai suna Marbin Hajos mai shekara 75, wani ne ya yi kiran gaggawa domin a kawo wa  Marbin dauki ta lambar 911 ga ofishin jami’an taimakon gaggawa na Karamar Hukumar Alachua, inji Shugaban ayarin jami’an Laftana Joshua.

An kai Marbin Hajos zuwa wani asibitin mafi kusa inda a can ne ya rasu, inji shugaban jami’an. Wannan tsuntsun ya kasance mallakin Marbin kamar yadda hukumomi suka yi binciken tsautsayin da ya faru a tsakanin Marbin da tsuntsun.

Mataimakin Shugaban Hukumar Kashe Gobara ta Karamar Hukumar Alachua, ya ce Marbin yana kiwon tsuntsaye ne kuma dan asalin kasar Austireliya.

Daya daga cikin jami’an mai suna Taylor ya ce, mutuwar Marbin wani tsautsayi ne da ya faru. Hukumar adana dabbobin daji da kifi ta Jihar Florida, ta fitar da rahoton cewa, irin jinsin tsuntsayen cassowary suna da hadari ga al’umma don haka ake bukatar a killace su a keji. Hukumar ta ce, masu rike da irin wadannan dabbobi ya zama wajibi a ce suna da wata basira ta hanyar kiwonsu.

Wannan tsuntsu na cassowary na da jinsi daya da kadoji da damisa har ma da irin jinsin su zakuna da dai wasu dabbobi masu hadarin kiwo.

A cewar Ma’aikatar Gidan Adana Dabbobin Daji ta San Diego, tsuntsun cassowary yana da girma kuna ba ya tashi sama, amma kuma yana iya tsallen mita  7, kuma zai iya gudun mil 31 a awa daya, sannan zai iya yin nikaya  yayin da zai kare kansa daga barazanar sauran dabbobi.

Tsuntsun zai iya girma sama tsawon kafa 5, macen tsuntsun za ta iya kai nauyin kilo 72.5748 yayin da namijin tsuntsun zai iya kaiwa nauyin kilo 54.4311.

“Wannan tsuntsun cassowary ana bayyana shi da tsuntsu da ya fi hadari a duniya,” kamar yadda gidan adana dabbobin ya sanar. Kowane farcensa ya kai tsawon inci 4, zai iya illata duk abin da yake son ya ga bayansa a lokaci guda.