✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tuba ga Allah ne babban maganin annoba – Gwamna Masari  

Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari, ya ce babban maganin kowace irin annoba shi ne komawa ga Allah tare da yin tuba gare shi.…

Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari, ya ce babban maganin kowace irin annoba shi ne komawa ga Allah tare da yin tuba gare shi.

Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake yi wa al’ummar jawabi akan bullar cutar Conorovirus da ke neman zama ruwan dare. Gwamnan ya ce, ita wannan cuta bata da babba ko yaro bare nau’in fata da sauran su.

“Kasashen da masu halin mu suke zuwa domin duba lafiyar su, kamar irin su Amurka, Ingila da sauran su yanzu su ma suna gudu akan wannan cuta.“

Saboda haka, muke ta kokarin daukar matakan kariya musamman na fitar da wasu cibiyoyin kiwon lafiya wadanda nan ne matakin farko sai in abin ya fi karfinsu sannan su zo babban asibiti wadda a nan za a dauki jini domin zuwa cibiyoyin Abuja ko Legas da ke da manyan na’urar binciken cutar.

Gwamnan Jihar ya kara da cewa, gwamnati na kira ga manyan masu shagunan sayar da kaya da suyi kokarin samar da sinadaran da ake shafawa ga hannuwa tare da wasu na’urorin gwajin da ba wata tsada gare su ba, domin yin amfani da su ga abokan huldar su. “Zamu sanya jami’an tsaro su bi irin wadannan shaguna domin ganin suna amfani da wadannan kayan kariya.

Sannan muna kira ga jama’a da su rage yawan taruwa a wuri daya in ba bisa wata lalura mai karfi ba, ko anan ma kada a wuce mutane 30. Sannan ina kara kira ga jama’a da cewa mu tuba mu koma ga Allah, ita kadai ce babbar hanyar kuma maganin kowace irin cuta ko annoba a tsakanin al’umma, in ji Gwamna Masari.