Search
Subscribe
Tube Sarki Sunusi II: Gwamnoni ke tsoma sarakuna a siyasa – Shehu Gabam

Alhaji Shehu Musa Gabam

Tube Sarki Sunusi II: Gwamnoni ke tsoma sarakuna a siyasa – Shehu Gabam

Alhaji Shehu Musa Gabam shi ne Sakataren Jam’iyyar SDP ta Kasa, wanda kuma ya tsaya wa jam’iyyar takarar Mataimakin Shugaban Kasa a zaben da ya gabata. A tattaunawa da wakilinmu, ya ce tube Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II da Gwamnatin Jihar Kano ta yi babbar cutarwa ce ga Arewa:

Me za ka ce game da tube Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II da gwamnatin Jihar Kano ta yi?

To da farko dai babban abin bakin ciki ya faru ga mutanen Kano da mutanen Arewa, kan sauke Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II  da gwamnatin Jihar Kano ta yi. Kuma ya kamata duk wani mai kishin Arewa da son ci gabanta ya yi bakin ciki da faruwar wannan lamari. Babu shakka tube Sarkin daga sarautar Kano ba karamin cutar da Arewa zai yi ba.

Yau a Arewa shi kadai ne Sarkin da ke fitowa ya yi magana. A duk inda ya je a duniya ya yi magana sai an tsaya an saurare shi, bai cutar da al’umma ba, don haka bai kamata a wulakanta shi ba.

Da farko an zarge shi kuma ya tafi kotu, kuma kotun ta bukaci a dakatar da wannan abu. Ya kamata a bari a gama shari’ar, idan an same shi da laifi sai a dauki mataki na hukunta shi.

Kuma abin takaici kan wannan lamari manyanmu sun zauna sun yi shiru. A Arewa akwai manyan malamai da sauran shugabanni amma sun yi shiru, sun bari an tozarta mutumin da ke cikin fitattun mutanen da ake ji da su a fannin ilimi a duniya.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya san da wannan magana, amma ya ki ya sanya baki a matsayinsa na shugaban Arewa kuma shugaban Najeriya baki daya.

Bai kamata mutanen Arewa su kara barin wani Gwamna, ya kara tozarta wani Sarki a Arewa ba.  Wannan abu da aka yi, ba wai Sarki Sunusi aka yi wa ba, Masarautar Kano aka tozarta wadda duk Arewa ana ji da ita. A duk duniya idan ka yi maganar Masarautar Kano, ka yi maganar Najeriya ce.

Yaushe ne mu ’yan Arewa muka lalace muna tozarta kanmu da iyalanmu da matsayinmu a duniya? Mu da a da aka sanmu da rike amana da mutunci da gaskiya.  Me ya sa muka lalace muka zama yau a Arewa mu ne muke hassada ga junanmu da tozarta junanmu? Me ya sa muka kasa biya wa ’ya’yanmu kudin makaranta, muka kasa samar musu da ayyukan yi? A yau ’yan Arewa ne suke kashe ’yan Arewa, gaskiya lalacewarmu ta kai lalacewa.

Me za ka ce kan zargin da wadansu suke yi wa sarakuna na shiga harkokin siyasa?

Duk sarakunan Najeriya gwamnoni ne suka sanya su a siyasa. Domin gwamnoni suna kiran sarakuna su ce ku je ku fada wa hakimanku da dagatanku cewa ga wanda za a zaba. Idan kuma ba su zaba ba, za su samu matsala. Duk gwamnonin Najeriya suna yin haka, don haka gwamnoni ne suka sanya sarakuna a cikin siyasa.

Kuma wani abu da zan fada duk Gwamnan da yake son a yi zaman lafiya a jiharsa, za a yi. Domin duk Gwamnan da yake son ya samu labarin duk abin da ke faruwa a jiharsa, zai iya samu. Zai iya sanin wadanda suke kawo fitina da satar mutane a kauyukan da ke jiharsa. Amma ba sa son su kashe kudaden jihohinsu wajen gano irin wadannan abubuwa, sun fi son su kwashe kudaden su fita da su, su je su rika jin dadi su da iyalansu, ta hanyar sayen manyan motoci da manyan gidaje. Sun bar mutanen jihohinsu cikin fitina da bala’i, suna tunanin Allah ba zai tuhume su ba.

To, a nan wane kira ne kake da shi ga gwamnonin Arewa game da wannan lamari?

Gaskiya gwamnoninmu na Arewa su yi hattara, domin tarihi da hakkin al’ummar Arewa zai bi su, kan yadda suna ji suna ganin Arewa tana ci gaba da tabarbarewa. Babu makaranta babu aikin yi, sannan mu zo shugabanninmu sarakunan Arewa wadanda cikinsu akwai wadanda Allah Ya yi wa baiwa, duk duniya sunansu ya fita, amma a ce yau saboda wani bambanci na siyasa su ne muke tozartawa.

To na farko dai babu mai gadon kujerar Gwamna ko sanata ko dan majalisar wakilai ko kansila. Duk wanda ya nemi wadannan kujeru, idan Allah Ya ba shi zai samu. Amma masarauta tana da tarihi tana da gado. Don haka saboda me za mu lalata masarautummu, don al’umma sun zabe mu Sarki yana karkashinmu, sai mu zo mu tozartasu?

Idan Gwamna ya sauka daga mulki gobe, ya san yadda Allah zai mayar da shi? Akwai tsofaffin gwamnoni da suka sauka, suna neman inda za su sa kansu yanzu.

Yaranmu sun koma shaye-shayen miyagun kwayoyi da garkuwa da mutane da fashi da makami. Gaskiya mun ji kunya kuma muna kan jin kunya.

Wannan abu da ya faru zai iya lalata masarautunmu na Arewa domin kowanne Gwamna idan bukatarsa ta taso, zai je ya samu Sarki ya tozarta shi, ko ya lalata masarautar.  Ban taba ganin Sarki Sunusi II ba, ban taba magana da shi ba. Amma yadda muke son mu kawo wa kanmu zalunci a Arewa, wallahi babu wanda zai tsira. A ce mu da aka sanmu da iya mulki, amma yanzu mun kasa iya hada kan mutanen Arewa, gaskiya mun ji kunya.

A yau saboda lalacewarmu ba mu da wani mutum guda a Arewa da zai fito ya yi magana matasanmu ba su fito a shafin sada zumunta sun zagi iyayensa ba. Babu abin da ya kawo mana wannan hali da muka shiga, sai rashin gaskiya da zalunci da rashin taimaka wa matasanmu su yi karatu. Kuma wannan duk laifin shugabannin Arewa ne.

Su marigayi Sardauna sun tafi da kowa sun hada kan al’ummar Arewa. Don me a wannan zamani muka kasa hada kan al’ummarmu na Arewa? Don haka sarakunan Arewa da malaman addini dole ne su tashi su hada kansu don a magance wannan matsala.

Don haka mu tashi mu kare masarautun Arewa, domin su ne kadai suka rage mana. Kuma shugabannin Arewa ya kamata su gane cewa mutuncinsu shi ne hada kan al’ummar Arewa, domin a dawo da martabar Arewa. Muna da yawan mutane, muna da masu ilimi. Yau idan ka dubi wadanda suke mulkin Najeriya Hausa, Fulani, Kanuri ne, su ne shugabannin tsaron Najeriya, amma yau su ne ake kashewa a Najeriya.

Shugaba Buhari ya taba fada a lokacin da yake yakin neman zabe, cewa abin kunya ne a ce a yi shekara biyar ana yaki da Boko Haram, a gagara magance su. To yau shi ma yana shekara ta biyar, yana mulkin Najeriya. Babu shakka hare-haren Boko Haram sun ragu, amma yawan mutanen da ake kashewa a yanzu, ya fi mutanen da ake kashewa a lokacin da Boko Haram suke kai hare-hare. Don me ba za mu fadi gaskiya ba, mu tsaya muna rufa-rufa muna cutar kanmu ana ta kashemu?

An kawo Buhari ne saboda ya ce zai yi adalci saboda a lokacin da yake Shugaban Kasa na soja, an yi masa rashin adalci an cire shi. A zaben da aka yi na farko da bai ci ba, ya rika yin kuka al’umma suka tausaya masa aka zabe shi. Ni na zabe shi, mahaifina wanda ya rasu mako biyu da suka gabata da shi muka je wajen zaben a lokacin yana da shekara 100. Na ce wa yake so ya zaba? Ya ce a nuna masa Buhari, ya ce ni ma in zabi Buhari. Me Buhari yake so mu yi masa, fiye da wannan? A kullum ana kashe mu, al’ummarmu ta shiga wani mawuyacin hali, a ce kada mu yi magana.

Buhari ya fada da kansa cewa yana mamakin yadda har yanzu wannan fitina ta tsaro ba ta kare ba. Don me yana Shugaban Kasa zai ce haka? Wane irin bayani  ne ba ya da shi a matsayinsa na Babban Kwamandan Askarawan Najeriya? Ya kamata yana da bayanin duk wadanda suke kawo wadannan matsaloli na tsaro a Najeriya.

Kafin ya zama Shugaban Kasa ya ce za su binciki duk wanda aka samu da hannu a rikice-rikicen da aka yi a Najeriya, domin a hukunta su, amma har yanzu ba a binciki kowa ba.

Dubi irin rikice-rikicen da suka ci gaba da faruwa a Najeriya, dubi irin talaucin da ya addabi mutane a Najeriya.

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin