✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tukwicin zaben 2015: Mu gyara halayenmu (2)

Ci gaba daga makon jiya Hakika mu ‘yan Nijeriya muna da bukatu masu yawa. Maganar tsaro ba sai na fada ba, da maganar ilimi. Ga…

Ci gaba daga makon jiya

Hakika mu ‘yan Nijeriya muna da bukatu masu yawa. Maganar tsaro ba sai na fada ba, da maganar ilimi. Ga kuma maganar hannyoyi, musamman jihohinmu da suke baya, a inda na sani, a Adamawa, akwai matsalar hanyoyi sosai, abin mamakin shi ne, shekara da shekaru ana ba da aikin gyaran hanya, amma sai a kasa karasawa, in kuma an yi hanyar, bayan wata 8 zuwa 10 sai a tarar ta lalace, laifin ko na wane ne, ba a ganewa. Hanyan shiga Yola daga Jimeta,guda daya tak, wani abu kadan na faruwa sai harkoki su tsaya cik.Da a ce akwai wata hanya ,da abin ba zai zama haka ba, da fan za a samu wasu hanyoyin amin. Hanya daga Yola zuwa Ganye,Yola zuwa Mubi,Yola zuwa Fufore, hakika suna neman gyara, talakawa suna shan wuya, musamman hanyar zuwa Ganye, da kuma ta Mubi.
Idan an ba da kwangilar babu masu lura da aiyukan ne? Ko kuma kudin da ake bayar wa ne, ba sa isa ? Allah ne masani. Wasu kuma bukatunsu, gada ce don akwai wani kauye, a karamar hukumar Jada ana kiran garin Sintali, a gundumar Kwajoli,idan lokacin damina ya yi, yara kanana ba sa zuwa makaranta, saboda akwai rafi a wajen. A wasu wuraren kuma,juji ne yake rufe hanya da kuma lambatu, abin ba kyan gani sam.
Na san jihohi da yawa,suna da irin wannan matsalar. Da fatan za a dawo da yaki da rashin da’a.
Wasu asibitocinmu abin tausayi ne,wasu wuraren katifun dake kan gadajen ma,abin kyama ne,ballantana ma a yi maganar kayan gwaje-gwaje,na dakin gwaji, duk babu su.A kullum sai dai a je a yi, a asibitin kudi, a kawo musu sakamakon. Muna fatan duk Janar zai sa a kula da su,idan an ba da kudin gyaran,a tabbatar da komai yana tafiya dai-dai, kamar yadda ya sa ba yi.
Wasu kuma matsalarsu, ta bangaren filin jirgi ne, masu tafiye-tafiye, suna kukan rashin tsari, da kuma rashin kula da filayen.Duk da arzikin da muke da shi, ga shi dai mutane suna biyan kudin duk inda za su je, amma ba su damu da gyara ba, ko kuma kyautata wa wasu fasinjoji masu larura ba, wadanda ba sa iya takawa su hau jirgi, sai dai a daga su, da wanda aka daga, da wadanda suka daga shi duk a wahale suke.Don haka suke son,gwamnati ta duba lamarin,ga duk wadanda suke da alhakin sayen na’urar da ake amfani da ita a kasar waje,ba sai mutane sun daga mutum ba. Watakila wasu za su ce, wannan ai ba shi ne damuwar ‘yan Najeriya ba, a yau in muna da lafiya, ba wanda ya san yadda zai kasance a gobe ba.
Wasu kuma tsadar gidajen haya ne matsalarsu.Domin masu karamin albashi, suna son yin aure amma sai su gagara,gida mai daki biyu ace (600,000) ko fiye da haka,wata unguwa ma har (1.300,000), yake kai wa.Suna kuma yawan kara kudi, albashin ma’aikatan kuma ba mai yawa ba ne, da zai ishe su, cin su da kuma shan su, har da za su tara wa,masu gidaje,wannan kudin. Da fatan Janar zai duba matsalarsu, in zai yiwu, ko a gina musu gidaje, kamar yadda ake yi a da, ko za a samu, saukin matsalar, don su san an samu canji.
Matasa da yawa, sun san Janar ne, lokacin da ya zama Shugaban hukumar tace rarar man fetur (PTF), yadda hukumar ta wadata kasa da aiyuka masu amfani, kamar gyaran hanyoyi da makarantu da asibitoci da sayo musu motoci da sauransu. Shi Janar a lokacin da ya yi Gwamna ya kuma yi Shugaban kasa, duka-duka shekarunsa ba sufi 41 zuwa 42 ba.A lokacin, duk da cewa akwai wadanda suka wawure kudin gwamnati a wancan lokacin, kafin ya hau. Da ya zama Shugaban kasa, ya daure su, sai da suka dawo da kudin,amma bai sa ya kwashe su ba, saboda ba ya son wawurar hakkin da ba nasa ba, don ya tara wa ‘ya’yansa dukiya, ko da ya sauka, su yi rayuwarsu cikin jin dadi da walwala, kada su talauce. Bai kuma yi, kishin aljihunsa ba, sai kishin kasa ya yi. Don haka nake son mu yi koyi da shi. A yanzu mutum nawa ne suke da irin halinsa, masu karamin shekaru kamar shi a lokacin,da kuma tsofaffi a Nijeriya a yau?.
A yadda muke ji a rediyo da kuma talabijin, na kusa da shi , suke yabonsa,wajen tausaya wa marayu, yake kuma bakin cikin ganin ya raba su zuwa makaranta, yakan tallafa wa, da yawa, don su samu su yi karatu.Har ila yau, an ce shi manomi ne, yakan raba wa marasa galihu abincin da yake nomawa,har aka ce wani lokacin yakan saya don ya rabar,yin haka yana da kyau, kuma bai sa ya talauce ya rasa abin da zai ci ba. Muna fatan masu yin irin wannan Allah ya kara musu kwarin gwiwa, marasa yi kuma, Allah ya ganar da su alfanun yin haka,masu sha’awar yi,Allah bai hore musu ba, Allah ya buda musu amin.
Wata matsala kuma,wadda Janar ya riga ya sani, ita ce maganar marayu, hakika kowa ya san mafi yawansu,suna tashi cikin matsala ne, ballantana wadannan jihohi da aka yi,tashe-tashen hankali. Mafi yawa daga cikinsu,ban da iyayensu da aka kashe,har ma da ma su daukar nauyinsu cikin dangi,dukkansu an kashe su, wasu kuma an kona dukiyoyinsu, babu damar su taimaka musu. Da fatan duk wanda Allah ya hore wa abin hannu,da ya taimaka musu, ba sai gwamnati ba, amin.
Muna kuma yi wa iyalan Janar da sauran ‘yan Najeriya, fatan Allah ya tabbatar mana da dukkan alkhairai, ya kuma hada mu a gidan aljanna amin. Shi kuma Farfesa Attahiru Jega Allah ya kare shi,daga dukkan sharri,kamar yadda ya kare mana kuri’ummu. Na tabbata yanzu ne martabar shi ta dawo kamar yadda aka san shi a da.
Dukkan matsaloli da muka ambata,ba lallai ne a ce na gwamnatin tarayya ne ba, mun san akwai na jihohi,har ma akwai na kananan hukumomi, amma muna son,a sa su cikin wadanda za a lura da su,bayan an ba da kudin aikinsu.
Asiya Musa
No.10 Amazing Grace
Gwagwalada,Abuja