✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tunawa da Sardauna Gamji Dan Kwarai

Talatar da ta gabata, 15 ga Janairu, rana ce da al’ummar Arewacin Najeriya ke tuna magabatan farko kamar Firimiyan Arewa Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato…

Talatar da ta gabata, 15 ga Janairu, rana ce da al’ummar Arewacin Najeriya ke tuna magabatan farko kamar Firimiyan Arewa Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato da Firayi Ministan Najeriya Sa Alhaji Abubakar Tafawa Balewa wadanda wadansu sojoji daga wani sashe na kasar nan suka yi wa kisan gilla, suka kuma jefa kasar cikin mummunan Yakin Basasar da ya yi sanadiyyar mutuwar sama da mutum miliyan daya.

Marigayi Sa Ahmadu Bello Sardauna ya sadaukar da rayuwarsa wurin kare mutuncin mutanen Arewa, tun lokacin da aka zabe shi wakili a Majalisar Dokokin ta Arewa da ta Kasa.

A duk mukaman da ya rike daga lokacin kama daga Ministan Ayyuka, Ministan Kananan Hukumomi, da shugabantar Jam’iyyar NPC, ba abin da ya sa a gaba illa yadda zai kare mutuncin Arewa daga makiyanta na wancan lokaci.

Duk tarurrukan rubuta kundin tsarin mulki da aka yi daban-daban a Ibadan da Legas da Landan, ya tsaya, tsayin daka wajen kare muradun Arewa. Arewa ba za ta manta da gwagwarmayar da aka sha a Majalisar Dokoki ta Kasa ba musamman batun lokacin da za a ba Najeriya ’yancinta.

Sa Ahmadu Bello ne ya kafa masana’antu da kamfanonin Arewa na farko a karkashin hukumomi ko kamfanonin NRDC da NNDC. Wadanda suka samar da Bankin Arewa,  da Kamfanin Siminti na Sakkwato da Kamfanin Sukari a Ilorin da kamfanonin yin sabulu da turare da kwanuka da robobi da otel- otel kamar Central Hotel a Kano da Hamdala Hotel a Kaduna da Kaduna Brewery da masaku wadanda NORTED ta assasa kamar Kaduna Tedtile, Arewa Tedtile, Zamfara Tedtile.Gina ’yan kasuwar Arewa domin su iya gogayya da mutanen Lebanon da suka mamaye kasuwanci.

A nan mutane irin su Haruna Kasim da Aminu Dantata da Isiyaku Rabi’u da sauransu, an ba su bashi da goyon bayan gwamnati.

Ta bangaren ilimi, an gina makarantun sakandare sama da hamsin, ya kafa NNPC wanda shi ne kamfanin da ke samar littatafai da jaridu da mujallu kamar Nigerian Citizens, Gaskiya Ta Fi Kwabo, New Nigerian da litattafai kamar Magana Jari Ce, Ruwan Bagaja da sauransu.

Lallai Arewa ba za ta taba mantawa da NORTHERNIZATION POLICY ba.Tsarin da ya yi kokarin rage tazara tsakanin Kudu da Arewa, inda wajen daukar aiki, ake la’akari da dan Arewa, in babu a dauko dan Kudu. A tsarin Northernization Sardauna ya ba da fifiko wajen horar da ’yan Arewa, wato crash training, Northernization ya taimaka kwarai wajen hana wadansu mutane danne Arewa.

Nada Sule Katagum  a Hukumar Daukar Ma’aikata ta Gwamnatin Tarayya ya taimaka sosai ga Arewa. Sai dai kash, yanzu wadanda ke ikirarin su ne shugabanninmu, ba su damu da Arewa ba. Ba su da kishin jama’a, wannan ya sa yankin ya zama wurin kyankyasar ’yan ta’adda, inda tambadaddu ke aikata kisan jama’a da sunan Boko Haram ce.

Yankin ya koma inda ake satar mutane a nemi kudin fansa. Daga Gwoza har Birnin Gwari daga Jibiya har Okene, sun watse, sun lalace saboda rashin tsaro. Kamfanin NNDC ya mutu, New Nigerian ta watse, Gaskiya Ta Fi Kwabo ta zama sai a dai a shafin facebook, Hamdala Hotel, Central sun cefanar sun sace kudin. Sun koma ba da kwangila ga ’yan korensu, suna karbar kashi 10. Ba su daukar kowa aiki sai kannen matansu da kawalansu da ’yan barandar siyasarsu.

Taron Kungiyar Gwamnonin Arewa ya koma ihunka-banza, sai an yanka mutane kan kwalta, sannan a zo a tattauna, a yi hira marar amfani.

Allah Ya kawo lokacin da mutanen Arewa za mu farka daga barci mu dawo cikin hayyacinmu.

 

Kwamared Bishir Dauda Sabuwar Unguwa Katsina

Babban Sakataren Kungiyar Muryar Talaka ta Kasa. 08165270879