✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tuntun tagiyar Tunau (1)

By [email protected] Tuntun tagiyar Tunau kasurar kosau Kurarin kwarwar Korau Make-maken Makau Salallamin Sallau Tamke tanka tamau Kinkimar kwarin kibau Mikakken mashin Misau Tuttudo na-mujiya…

By [email protected]

Tuntun tagiyar Tunau

kasurar kosau

Kurarin kwarwar Korau

Make-maken Makau

Salallamin Sallau

Tamke tanka tamau

Kinkimar kwarin kibau

Mikakken mashin Misau

Tuttudo na-mujiya da tabarau

Bankwarewar barewar Barau

Kayan karau

Kame-kamen Kumayau

Karambanin kambamau

Gumurzun Gwmana el-Rusau

Rarume-rarumen  Runtumau

Jaye-jayen Jatau

Matashiyar Malam Mantau

Kumburin karambau

Sankarewar sankarau

Janjamin uwar jiki kalau

Jimurau

Abokin Barau

dundume tumbin kumburau

Taunar gyada marau-marau

Gwale na-mujiya garau

Damben danniyar Dannau

Suddabarun sagewar Sagau

Sullutun sakarcin Shashatau

Sagaraftun sunkurun sungumau

Mulkin mulaka’un Makasau

Azargagiyar zargau

Zanzarewar Zarau

Mai tseren fintinkau

Jiya da yau

Malam ya cilla kibau

Masu ra’ayin rikau

Gurguzun gazawar gezau

Kwamunisancin kwansau

Jari-hujjar hajijiyau

Fahimtar fankan-fayau

Gungumen gingimen ginsau

Gangaren gagarau

Gararambar ganau

Gantsare-gantsaren gantsarau

Gingimarin gangarau

Wasan kwaikwayo

Gogen Garba Liyo

Malam koyi ka kara koyo

Batutuwa ne aka liliyo

In an ga wuya sai a mazayo

Ni dai na tafi in tambayo

Masu bita a bibiyo

’Yan wanki a daurayo

Masu zirga-zirga a zagayo

Kogin fundun-fundun ai iyo

Lallai a waiwayo

Akuya kar ki tunkuyi kwikuiyo

Rairayi aka rairayo

‘Baagadoji’ indar kewano ta kewayo

‘Bago’ babu ‘biri’ a tsinkayo

‘Shigifar ga’ na yoyo

Marka-marka ya tsiyayo

Gulbi ne ya antayo

Goriba aka gwagwiyo

Handamar miyagu a amayo

Uwa ta tamke majanyin goyo

Kan jariri ya juyo

Ka da a bari ya lankwayo

A  muskuta a sunkuyo

A hau sululun Saliyo

Tsiyataku

kullin kutu-kutu

Surutu rututu

An yi shigar burtu

Ana tsikari da tuntu

A duba wanga batu

Wasu na ta babatu

Da masu sambatu

Zobarar zunbutu

Ko wasu sun zautu

Talo-talo

Santolo

Mai fuka-fuki falo-falo

Yana taku salo-salo

Wuyansa  kamar na zololo

Jan ragama

Ko juyayin rigima

’yan adawa na ta tsima

Suna ta hauma-hauma

Don rashin sanin makama

Akwai ’yan takara

Da masu taka-kara

kuri’unmu sufe safara

Don su haifar wa kasa asara

Su ke daukar nauyin suka-da-sara

Wai Baba kar ka tsaya

An gaji da sharar tsintsiya

Don ta share ’yan tsiya

Da suka jefa jama’a wuya

Miyagu na  cusa kiyayya

Don su nunke mu a baibai

Su musanya Hauro a baibai

Sun kwashe matsabai

Zamanin da babu kwabbai

Zirga-zirgar ziryar zuwa Dubai

Baba ya taka musu burki

Ya ce a rage bariki

A yi aikin kirki

Masu sana’ar na-duke ga taki

Dami ya fi kayan jaki

Kun dauke ni hutsu

Halin aura ne tutsu

Fur shi ne tashin tsuntsu

In an ji ana mutsu- mutsu

Za a ji tsuwwa tsu-tsu

Sasarin sakarcin sakarai

Langabun lalurar Larai

Jiniyar jinjiniyar jarirai

Bilinbituwar birai

Loton laftun labarai

Dama-damar daurin dammai

Masu fafutikar  neman mukamai

’Yan jagaliya an jawo makamai

Don lasar maskin maikon mai

Amma ba manufa takamaimai

Juriyar jarumi jarmai

Jimamin Jimmai

Ja-in-jar jama’a ai-ai

Aikin jinkai

Don kawar da kaikai

Kimiyyar sarrafa sinadarai

Kwaba magungunan Bokan Turai

dan magori mai tarairaya rai

Ruwan magani garai-garai

An ga amfaninsa sarai

Haurobiyawa ka da ai butulci

Mui wa Baba karamci

Yai mana fafutikar ’yanci

A cire wa al’umma sasarin kunci

Lallai ka da mui sokwanci

An fasko masu kirinki

Da ke hana aikin kirki

Suna sunna wa ’yan baranda sunki

Su banka wa jama’a buki

Da tutiyar kulle-kullen daki

Dagirgiri

Dogarawan dogari

Dundumin dumamar gari

Dungun dungurar garari

Dama-damar daurin danmari

Baban-burin-huriyya

kara kokarin gina Haurobiya

Ka kiyayi masu waskiya

Masu ta’adar danniya

Da suka kware a nuna wariya

Al’umma ta nuna juriya

A karkashin mulkin mai tsintsiya

’Yan zagon kasa na ta tsiya-tsiya

’Yan adawa na ta makircin kuliya

A hada karfi da karfe don kariya

A dabbaka kyawawan ta’adu

Sai kasarmu tai tsiran tudu

A shawo kan gada-gadar gudu

Kwashi-kwaraf inna rududu

Mu dabi’antu da awon mudu

Ni dai ina ba da sautu

Tagiyata na da tuntu

Ina masu buruntu

Kwaramniyarku ta fi surutu

Kun maishe da kowa sullutu

A fifita adala

Kan laluben dala

Don kauce wa masu dafdala

Masu aikin juhala

Fa’idar ka’ida na sa a daina lalala!