Aminiya

Turawa na mana gori kan ba mu ba ilimi muhimmanci  – Farfesa Gbajamila

Farfesa Ibrahim Gbajamila Shugaban Jami’ar Crescent, Abeokuta

Farfesa Ibrahim Gbajamila shi ne  Shugaban Jami’ar Crescent da ke Abeokuta.  Shehin malami ne da ya taso a Ingila inda ya yi karatu tun daga firamare ya kuma  shafe sama da shekara 30 yana koyarwa da yin nazari a Jami’ar Landan a Birtaniya kafin ya komo Najeriya. A zantawarsa da Aminiya ya fadi dalilinsa na komowa gida da kalubalen da kasar nan ke fuskanta a fannin ilimi da hanyoyin da ya kamata a bi domin inganta ilimi a kasar nan:

 

ADVERTISEMENT

Zamu so ka gabatar da kanka

Farfesa Gbajamila: Suna na Ibrahim Gbajamila, ni ne Shugaban Jami’ar Crescent da ke Abeokuta mai zaman kanta. An haife ni a cikin zuriyar Gbajamila da ke Legas wadanda suka shahara a fuskar ilimi da kasuwanci da siyasa. Mahaifana sun ta fi da ni kasar Ingila tun ina karami, a can na yi karatun firamare zuwa digirin digirgir a fannin kimiyyar kwayoyin halitta  har na zama Farfesa a Jami’ar Landan inda na shafe sama da shekarA 30 ina aikin koyarwa da nazari.

ADVERTISEMENT

Mene ne  dalilin dawowarka gida Najeriya?

Farfesa Gbajamila: Na dawo gida Najeriya ne domin in bada gudunmawa wajen bunkasa ilimi a kasata, mahaifina malamin makaranta ne haka shi ma wanda ya haifi shi wato kakana, wanda shi ne ya kirkiro kungiyar Ansaruddini a Unguwarmu da ke Isaleko a Legas.Kungiyar da ta kafa makarantun firamare da sakandare masu yawa a jihohin Kudu maso Yamma, a dalilin wadannan makaratu al’ummar yankin sun samu damar tura ’ya’yansu karatu wadanda su ne suke jan ragamar al’amuran yankin tare da ciyar da shi gaba domin babu abin da za ka yi kamar gina al’umma fiye da ba su nagartaccen ilimi. Na fara sha’awar dawowa gida ne lokacin da na hadu da Yarima Bola Ajibola a Inglila wanda shi ne ya asassa jami’a mai zaman kanta ta Crescent. A lokacin da muka hadu, shi ne Jakadan Najeriya a Ingila, shi ya jawo ra’ayina kan in dawo gida in bada gudunmawata domin mu taimaki sha’anin ilimi a kasarmu. Ya bayyana min cewa a wancan lokaci duk sa’ar da ya je zaman kotu a kasar ta Ingila a matsayinsa na babban alkali idan ya gabatar da kansa a matsayin dan Najeriya Turawan kan yi masa shagube suna cewa ya zo daga kasar da ba ta bai wa sha’anin ilimi muhimmanci. Ya ce an sha fada masa irin wannan sau da dama wannan shi ne dalilin da ya zaburar da shi har ya kafa rukunin makarantu tun daga matakin nazare har zuwa jami’a a birnin Abeokuta. Wannan hazikin dattijo ne ya sauya min tunanina na baro kasar Ingila na dawo gida domin ni ma in bada tawa gundunmawar

Me ya sa kasashen Turai ke ganin an bar mu a baya ta fuskar ilimi?

Farfesa Gbajamila: Tabbas haka abin yake, an bar mu a baya ta fuskar ilimi domin kashi 20 na yaran da ba sa zuwa makaranta a duniya a Najerya suke, kuma a yanzu ma al’amuran kara tabarbarewa suke yi, wannan lamari yakan tada min hankali. A 1995 Majalisar Dinkin Duniya ta ba mu dama mu gyara amma haka lamarin yake a shekarar 2005 ba a samu sauyi ba, lamarin ma ya kara kazanta a shekarar 2015, idan ka duba kasashen Afirka irin su Ghana da Tanzaniya da Zambiya suna samun ci gaba sossai duk da su kananan kasashe ne da ba su kai mu yawa da karfin tattalin arziki ba, a duniya Najeriya ce ta 10 a fagen samar da danyen man fetur amma har yanzu mun kasa amfani da dimbin arzikin kasa mu inganta ilimi. Haka kuma mu ne koma-baya ta fuskar kiwon lafiya domin a duniya a kasar nan ne aka fi samun yawan mutuwar yara kanana, wadannan matsaloli ne da suka kamata kowa ya yi tunanin bada tasa gudunmawar domin kawar da su

Ta wace hanya kake ganin za a iya inganta ilimi a Nijeriya?

Farfesa Gbajamila: Sai gwamnati ta sauya salon rikon da take yi wa fannin ilimi, ta  shiga a dama da ita a kowane fanni na koyo da koyarwa. Idan ka dubi jami’o’in da muke da su a kasar nan ba su da isassun gurabin karatu da za su dauki daliban da ke son yin karatu a jami’a. Kasa da kashi 30 cikin 100 ne ke samun guraban karatu a jami’oin kasar nan duk shekara. Shin kana tambayar ko me ke faruwa da kashi 70? Da yawansu kan shiga wani hali wannan shi ne ya sa wadansu mutane ke zuwa kasashen makwabtanmu suna kirkirar cibiyoyi bayar da takardun digiri na bogi kuma yanzu haka ’yan kasar nan da dama sun fada tarkon irin wadannan mutane,  z aka ga yaro ya tafi  Jamhuriyar Benin cikin kasa da wata takwas ya dawo da sunan ya kammala digiri. Irin wadannan makarantu na yaye baragurbin dalibai da ba su da kwarewa wadanda kan dawo su zamo illa ga kasa, me kake ganin zai faru idan irin wadannan makarantu sun yaye daliban da za su yi aiki a cibiyoyin lafiya ko bangaren gine-gine a irin haka me za ka ga ana samun jami’in kiwon lafiya masu hallaka al’umma maimakon agazawa ta fuskar lafiya, ko kuma jami’an gine-gine da ba su da kwarewa wadanda ke janyo rushewar gidaje suna hallaka jama’a. Don haka ya zama wajibi gwamnati ta shigo cikin wannan lamari sannan ta rika kokarin tallafa wa jami’o’i masu zaman kansu na cikin gida domin a kasarta suke, tana da ikon bincike a kansu tare da sanin yanayin da suke gudanar da aiki. Idan gwamnati ta tallafa wa jami’o’i masu zaman kansu za a rage yawan kudaden da ’yan kasar nan ke kashewa a jami’o’in kasashen ketare, domin a yanzu  kudaden da iyayen yara ke kashewa a jami’o’in da ke kasar Ghana kadai sun fi karfin kasafin  kudin da gwamnati ke ware wa sashen ilimi a kasar nan.

A naku bangaren mai kuke yi don ganin sha’anin ilimi ya bunkasa?

Farfesa Gbajamila: Alhamdulillahi kamar yadda na fada maka Cif Bola Ajibola mutum ne da ya himmatu don ganin an samu ci gaba a bangaren ilimi, wannan ne ya sanya ya kafa makarantun da na ambata  zuwa Jami’ar  Crescent a Abeokuta, yanzu haka jami’ar na shirin bikin cikarta shekara 11 da kafuwa. Kuma ta cimma manufa da dama a bangaren karatu a tsangayoyi da dama wadanda suka hadar da sashin shari’a, aikin jarida, kimiyya sinadarai da sauran fanonni, sannan muna da tsarin karatu na ma’aikata  da ake yi a karshen mako, da kuma tsarin da zai bai wa masu karatu da shaidar babbar diploma ta kasa samun shaidar karatun digiri bayan sun yi karatu a zango karatu na shekara biyu. Sannan yanzu haka muna shirin bude tsangayar karatun kasuwanci da ciniki  kwatakwacin wadda Alhaji Aliko Dangote ya gina a Jami’ar Bayero da ke Kano. Kuma ba da jimawa ba za mu bude tsangayar koyar da aikin asibiti fannin da ya shafi aikin karbar haihuwa, jinya da makamantan haka. Duk da yake jami’a ce mai zaman kanta amma muna sassauta kudin makaranta ta yadda masu karamin karfi za su amfana. Idan gwamnati ta shigo cikin wannan tafiya tamu za a samu damar taimaka wa al’umma. A baya gwamnatocin jihohin Kano, Sakwato, Zamfara, Legas da sauransu sun kawo dalibansu nan kuma an samu da yawa cikin daliban da suka nuna kwazo da bajinta. Muddin za a rika samun irin wannan ilimi zai inganta a kasar nan.