Da Dumi Dumi

Turkiya na safarar makamai ga Boko Haram?

A ’yan kwanakin nan ne wani gidan Talabijin  da ke kasar Masar mai suna ‘TB Ten’ ya nuna wani rahoto da mai gabatarwa ya saka wata murya wacce a ciki ake tattaunawa tsakanin Mustapha Barank, Ministan kimiyya da masana’antu na kasar Turkiya da Mehmet Karatas, Manajan Kamfanin Jiragen  Saman Turkiya a kan yadda za a yi jigilar makamai ga kungiyar Boko Haram daga kasar ta Turkiya.

Muryar  ta yi kama da wacce aka rawaito tun cikin 2014, a lokacin Barank, yana babban mai ba da shawara ga Shugaban Kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan, a tsakanin shekarar 2011 zuwa 2018.

Ramond Ibrahim dan kasar Amurka a cikin wata takarda da ya gabatar ya bayyna cewa wata kullalliya ce da kasar Turkiya ke shiryawa,  wacce kasar Musulmi ce, domin a kaddamar da kisan kare dangi ga Kiristoci a Najeriya.

Dole mu yi duba na tsanaki  a kan hakikanin abin da yake faruwa  a Gabas Ta Tsakiya, domin kasar Turkiyya ra’ayinta ya sha bamban da na rikicin da yake faruwa a Gabas Ta Tsakiya, duba da yadda take fama da kasashe a ciki da wajen yankin dangane da rikicin, wanda ake yunkurin bata kimarta. Amma  wannan ba shi ne karo na farko da ake samun rahotanni a kan kasashen da suke taimaka wa Boko Haram da makamai da kuma kayan aikin yau da kullum ba. A ’yan shekarun baya, an wallafa wani rahoto da ya bayyana cewa Gwamnatin Najeriya ta kwace wasu makamai masu tarin yawa a tashar jiragen ruwa da ke Tin Can Inland a Jihar Legas, wadanda aka shigo da su daga kasar Iran. Hakazalika, akwai wani dan kasar Faransa da aka rawaito shi yana cewa kasar Faransa tana da hannu  a kungiyar ’yan ta’adda ta Boko Haram kuma tana taimaka musu da makamai da kuma kayyakin gudanarwa da kuma ba su horo a makwabtan kasashen  da suka yi wa mulkin mallaka.

A iyakar saninmu, babu wani zargi a kan wannan tallafi da ake ba kungiyar Boko Haram da aka taba bincika kuma aka bayyana sakamakon ga al’umma. Yadda Boko Haram suka jima suna cin karensu babu babbaka, ba zai yiwu ba a ce babu wani tallafi da suke samu daga kasashen ketare. Sannan kuma rahotanni daga sassa da dama sun tabbatar da cewa makaman da suke hannun kungiyar Boko Haram sun fi na jami’an tsaron Najeriya inganci da dacewa da zamani. Sannan kuma a filin daga, sun fi sojojin Najeriya kwarewa da dabarun yaki na zamani, wanda suna samun jagoranci yadda suke yakar sojojin Najeriya daga kasashen ketare.

ADVERTISEMENT

Mun lura da cewa manyan masana’antun duniya masu kera makamai sun zama kamar wani dandali, wanda duk wadannan rukunin kasashe suke cin kasuwarsu. Wannan sabuwar takaddama da ta fito, wacce ta kunshi wasu daga cikin masu rike da madafun iko a Turkiya da kuma wasu ma’aikatu na kasar, yana nuna cewa lallai akwai baragurbi a cikin Gwamnatin Turkiyar. Kididdiga ta nuna cewa duk inda ’yan ta’adda suke kamar Boko Haram, yana bayar da dama ga safarar makamai sakaka, ba ka’ida.

Sabon rahoton da ya fito a kan alakanta Turkiya da safarar makamai ga kungiyar Boko Haram, abu ne da ya kamata a yi bincike na tsanaki, sannan a fito da rahoton binciken da aka yi ga al’umma, domin kowa ya sani. Bai kamata a ce an bar wannan zargin ya bi ruwa a banza ba, kamar yadda ya faru a baya. Kodayake har yanzu ba a kai ga tabbatar da lamarin ba amma duk da haka muna yabawa ga kalaman Daraktan Watsa Labarai na Rundunar Sojojin Najeriya, Birgediya Janar Onyeama Okechukwu, cewa sun dauki batun da muhimmancin gaske, sun sanar da dukkan hukumomin tsaro domin tabbatar da tsaron kasa.

Kodayake Gwamnatin Najeriya tana amfana da dangantakar da ke tsakaninta da Turkiya  a dukkanin bangarori, ba za mu so wannan dangantaka ta wargaje ba da sunan bincike. Amma ko don sake ci gaba da kyakyawar alakar da take tsakanin Najeriya da Turkiya ta karu, za mu so a binciki wannan al’amari tare da ita kanta kasar Turkiya, domin a yanke shakkun da ke tsakani. Turkiya ita ma tana fama da radadin ’yan ta’adda kamar yadda Najeriya take fama da su, suna fama da kungiyar Kurdawa masu dauke da makamai a ciki da wajen kasarta. Sannan kuma muna fata Gwmnatin Turkiya karkashin jagorancin Shugaba Erdogan, za ta duba irin kyakkyawar alakar difilomasiyyar da ke tsakaninta da Najeriya, da ta ba da hadin kai ga mahukuntanmu wajen tabbatar da binciken wannan al’amari.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya