Da Dumi Dumi

Turkiyya da EU sun tattauna kan ’yan gudun hijirar Syria

A farkon makon nan ne Shugaban  Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya gana da mahukuntan Kungiyar Tarayyar Turai (EU) a birnin Brussels, inda ya bukaci kasar Girka ta bude kan iyakarta domin bai wa ’yan gudun hijirar Syria damar kwarara zuwa Turai .

Tun gabanin ganawar, Mista Erdogan ya gabatar da jawabi a birnin Istanbul, inda ya bayyana cewa, zai gana da hukumomin Kungiyar Tarayyar Turai a farkon mako a kasar Beljiyum.

Shugaban ya tattauna da mahukuntan Turai  ne kan batun shige-da-fice bayan Turkiyya ta bude kan iyakarta, yana mai fatar cewa, zai dawo daga Beljiyum da mabambantan sakamako.

Matakin da Turkiyya ta dauka na bude kan iyakarta, ya dada rura tankiyar da ke tsakaninta da Kungiyar Tarayyar Turai, baya ga musayar zafafan kalamai tsakaninta da Girka.

Shugaba Erdogan ya gana da Shugaban Majalisar Tarayyar Turai, Charles Michel da kuma Shugaban Hukumar Turai, Ursula bon der Leyen a Brussels babban birnin Beljiyum.

ADVERTISEMENT

Mai magana da yawun Shugaban Majalisar EU, ya ce, shugabannin sun tattauna kan abubuwa da dama da suka shafi kungiyar da Turkiya da suka hada da batun shige-da-fice da matsalar tsaro da samar da zaman lafiya a yankin, baya ga lalubo hanyar warware rikicin Syria.

Turkiya dai ta sha yin korafi kan nauyin da aka jibga mata na kula da kimanin ’yan gudun hijirar Syria miliyan hudu da ke rayuwa a kasarta.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya