✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Turkiyya ta dage wa mata dokar dankwali ta shekara 90

Gwamnatin Turkiyya ta dage wa matan kasar dokar daura dankwali, wadda aka kakaba musu tsawon shekara 90 da suka gabata; a karkashin dokar mata ba…

Matan Turkawa na murnar dage dokar dankwalii ta shekara 90 da aka kakaba musuGwamnatin Turkiyya ta dage wa matan kasar dokar daura dankwali, wadda aka kakaba musu tsawon shekara 90 da suka gabata; a karkashin dokar mata ba za su daura dankwali su shiga makaranta ko ofisoshin gwamnati ba.
Wannan doka ta shekara 90, ta kange mata da yawa a Jamhuriyar Turkiyya daga shiga aikin gwamnati. Sai dai masu ra’ayin da ba ruwansa da addini na kallon dage dokar a matsayin shirin gwamnati na tabbatar da boyayyar akidarta ta Musulunci.
Hukumar Shari’a da rundunar sojoji nakasar sun amince da dage dokar, sannan an bugata a mujallar gwamnati ta ‘gazette.’
Wannan tsohuwar doka an kakaba wa mata ita ne a shekarar 1925, zamanin da Shugaba Kamal Ataturk ya bullo wa kasar tsarin sanya tufafi, wadda ta hana ma’aikatan gwamnati sanya suturar da ke da alaka da addini. Shi kuwa Erdogan ya bayyana cewa kawar da dokar wani bangare ne na “garabasar dimokuradiyya.”