✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Turkiyya ta fara kai wa Kurdawa hari ta sama a Syria

Jiragen yakin sama na Turkiyya sun fara kai harin bama-bamai a wasu sassan Arewa maso Gabashin Syria a yunkurin kasar na fatattakar mayakan Kurdawa daga…

Jiragen yakin sama na Turkiyya sun fara kai harin bama-bamai a wasu sassan Arewa maso Gabashin Syria a yunkurin kasar na fatattakar mayakan Kurdawa daga yankin.

A dai ce harin ya janyo mutuwar fararen hula, inji mayakan Kurdawan.

Turkiyya tana son kafa sansani  ne wanda za ta tsugunar da ’yan gudun hijrar Syria miliyan 3.6 da suka tsallaka Turkiyya, bayan ta fatattaki mayakan na Kurdawa.

Shugaba Donald Trump na Amurka ya janye dakarun kasarsa daga yankin, al’amarin da ya janyo masa suka a ciki da wajen kasar.

Ya kare janye dakarun da ya yi a ranar Talata, inda ya ce ba wai sun kware wa Kurdawa baya ba ne, inda ya bayyana su da ‘mutane na musamman’.

Kurdawa dai sun kasance kawayen Amurka wajen samun nasara a kan kungiyar IS a Syria.

To sai dai Turkiyya na daukar dakarun Kurdawan da suka mamaye rundunar hadin gwiwa ta Amurka a Syria (SDF) a matsayin kungiyar ’yan ta’adda.

Ana dai ganin janye dakarun Amurka daga yankin tamkar bai wa kasar Turkiyya dama ta far wa dakarun Kurdawan ne.

A ranar Talata ce Turkiyya ta bayyana cewa a shirye take ta fara yakin da ta dade tana shiryawa a Arewa maso Yammacin Syria, inda za ta rika kai hare-hare ga mayakan Kurdawa kawayen Amurka.

Wannan sanarwar ta zo ne bayan Shugaba Trump ya bayar da umarnin janye mayakan Amurka daga iyakar kasar.

Mista Trump ya sake kare wannan yunkurin nasa a ranar Talata inda ya bayyana cewa ba wai ya yanke hulda da Kurdawa ba ne.

A wasu jerin sakonni da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Mista Trump ya bayyana Turkiyya a matsayin abokiyar kasuwanci da kuma kawa ga kungiyar tsaro ta NATO.

Hakan ya zo ne sa’o’i kadan bayan ya ce zai lalata tattalin arzikin Turkiyyar idan kasar ta wuce ka’ida.

A martanin da Turkiyya ta mayar dangane da kalaman Mista Trump, Mataimakin Shugaban Turkiyya, Fuat Oktay ya ce kasar ba za ta bada kai bori ya hau ba idan dai kan batun shirin da take yi ne na yaki a Arewa maso Yammacin Syria.

A ranar Talata, Fadar White House ta tabbatar da cewa Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan zai kai ziyara Amurka ranar 13 ga watan Nuwamba bisa gayyatar da Mista Trump ya yi masa.

Me Turkiyya za ta yi a Syria?

A Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya na baya-bayan nan, Shugaba Erdogan ya gabatar da taswirar wani yanki mai fadin kilomita 480 da ba a yaki a iyakar Syria da yake so kasarsa ta kula da shi.

Yankin zai zama matsuguni ga ’yan Syria kimanin miliyan 3.6 da ke gudun hijira a Turkiyya.

A ranar Litinin Ma’aikatar Tsaron Turkiyya ta ce “An kammala dukkan shirye-shirye domin daukar matakin,” kuma kafa irin wannan yankin na da “muhimmanci” ga ’yan Syria da kuma samar da aminci a yankin.

Sai dai Turkiyya ta sha yin barazanar kai hari a kan mayakan Kurdawa a iyakokin Arewa maso Yammacin Syria.

Turkiyya na daukar ’yan sa-kan Kurdawa na YPG a matsayin wani reshe na haramtacciyar kungiyar Kurdawa da ta kwashe shekara 30 tana neman ballewa daga Turkiyya.

A wani bangare kuma a ranar Talata Iran ta bayyyana adawarta da duk wani matakin soji da Turkiyya za ta dauka a Syria.

Mayakan SDF na gudanar da wasu sansanonin ’yan gudun hijira da na rike iyalan wadanda ake zargin mayakan Kunigyar IS ce a ciki da wajen yanki mai aminci da Turkiyya ke bukata.

Ana rike da iyalan wadanda ake zargi mayakan IS a Ain Issa da Roj da ke cikin yankin.

Sansani mafi girma shi ne na Al-hol da ke kusa da iyakar Iraki, kuma yake da nisan kilomita 60 daga Tukiyya. Mutum dubu 70 ne ke sansanin Al-hol, kashi 90 dinsu mata da kananan yara ne, wadanda suka hada da mutum dubu 11, ’yan kasashen ketare.