Search
Subscribe
Turkiyya ta kama ’yar uwar al-Baghdadi

Abu-Bakr al-Baghadadi

Turkiyya ta kama ’yar uwar al-Baghdadi

Hukumomin kasar Turkiyya, sun kama ’yar uwar tsohon jagoran Kungiyar IS, Abu Bakr al-Baghdadi, wanda jami’an Amurka suka hallaka a makon jiya a wani hari da rundunar sojin ruwa ta musamman ta Amurka ta kai a Arewacin Siriya.

Hukumomin Turkiya sun kama yayarsa Rasmiya Awad da mijinta a yankin Arewacin Siriya da ke karkashin ikonta inda suke zaune tare da sauran danginta.

Gwamnatin Turkiyya dai na zargin matar wato Rasmiya Awad, mai shekara 65 da alaka da Kungiyar IS a cewar wan dan sandan ciki.

Jami’an leken asiri na Turkiyya sun ce mataki ne na tattara bayanai kan Kungiyar IS.

Bayan kama Rasmiyya da mijinta, an kuma kama surukarta da kuma wadansu yara biyar, inda manya daga cikinsu ke amsa tambayoyi. Turkiyya ta ce ta kama ta ce domin tatsar bayanai daga bakinta, yayin da kuma kasashen Yamma suka nuna shakku kan ikirarin Turkiyyar. Ko da yake kasashen Yamm sun amince za a iya tasar bayanai game da rayuwar Baghdadi da tsarin Kungiyar ISIS.

An kama su ne da yammacin ranar Litinin a garin Azaz da ke Lardin Aleppo na kasar Siriya.

Da ma dai yankin waje ne da Turkiyya ta sha kai wa farmaki musamman lokacin da take fatattakar mayakan Kungiyar IS da na Kurdawa a shekarar 2016.

Jagoran IS ya kashe kansa ne bayan samamen da dakarun Amurka na musamman suka kai a Arewacin Siriya, kuma a wani sakon murya da kungiyar IS ta fitar a intanet ta tabbatar da mutuwar jagoran nata tare da alwashin daukar fansa kan Amurka.

Baghdadi ya kafa daular Musulunci a Siriya a tsakanin shekarun 2014 zuwa 2017 kafin dakarun Amurka da Siriya da Iraki da na Kurdawa su tarwatsa IS. kamar yadda rediyon DW da BBC suka ruwaito

 

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin