✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Turkiyya za ta dakatar da kai hare-hare a Siriya

Turkiyya ta ce, ba ta bukatar ta koma kai hare-hare cikin Siriya, domin Amurka ta sanar da ita cewa, Kurdawan da ke Arewacin Siriyan sun…

Turkiyya ta ce, ba ta bukatar ta koma kai hare-hare cikin Siriya, domin Amurka ta sanar da ita cewa, Kurdawan da ke Arewacin Siriyan sun kammala janyewa daga yankin.

Kasar Turkiyya ta fidda wannan sanarwar ce sa’o’i bayan cikar wa’adin kwana biyar da ta diba na tsagaita wuta a hare-haren da dakarunta suke kai wa a yankin da ake masa kallon tudun-mun-tsira ne na Kurdawa a Arewacin Siriya.

Hakan na faruwa ne bayan wata ganawa da Shugaban Rasha Bladimir Putin ya yi da takwaransa na Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan a ranar Talata kan yadda za su samar da tsaro a kan iyakar kasar Siriya.

Shugaba Erdogan ya ce, “Wannan zaman tattanuwa zai zama wata dama ta maido da zaman lafiya cikin gaggawa, a yankin.”