✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Turmutsitsin aikin shiga da fice: Jonathan ya saka wa iyalan wadanda suka mutu

Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya umarci a soke daukacin sunayen wadanda aka dauka a aiki da Hukumar Shiga da Fici a ranar Asabar da…

Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya umarci a soke daukacin sunayen wadanda aka dauka a aiki da Hukumar Shiga da Fici a ranar Asabar da ta gabata.
Ministan Labarai Mista Labaran Maku ne ya bayyana haka a shekaranjiya Laraba bayan taron Majalisar Zartawa ta kasa, inda ya ce majalisar ta nuna bacin ranta kan mutuwar masu neman aiki da hukumar a yayin turmutsitsi.
Maku ya ce majalisar ta ji takacin aukuwar lamarin inda ta mika ta’aziyya da jaje ga iyalan wadanda suka mutu da wadanda suka samu rauni.
Ya ce Shugaban kasa ya ba da izinin a dauki ’yan uwan mamatan uku-uku a aiki da hukumar kuma daya daga ciki ta zamo mace, yayin da ya ce a dauki dukkan wadanda suka samu rauni a lokacin turmutsitsin.
Ministan ya ce Shugaban ya ba da umarnin a sake sabon daukar ma’aikatan shiga da ficin a wata rana da za a ambata nan gaba, kuma wani kwamiti a karkashin shugaban Hukumar daukar Ma’aikata na kasa ne zai gudanar da daukar aikin. Wakilan kwamitin sun hada da Kwanturolan Hukumar Shiga da Fici da wakilin Sufeto Janar na ’Yan sanda da na Kwamndan Janar na Hukumar NSCDC da na Daraktan Hukumar Tsaron kasa da na Hukumar Gidajen Yari da na Hukumar Kiyaye Haddura ta kasa.
Sai dai Maku ya ki amsa tambaya kan cire Ministan Cikin Gida Abba Moro daga kwamitin da kuma ko gwamnati za ta mayar wa wadanda suka biya Naira dubu daidai kudin rajistar neman aiki na baya ko kuma tana da niyyar kafa kwamitin da zai binciki abin da ya jawo mutuwar masu neman aikin.
Minista Abba Moro dai ya ce ba zai sauka daga mukaminsa ba, kamar yadda jama’a da kungiyoyi ke kiran ya yi saboda mutuwar mutane a turmutsitsin neman aiki da hukumar da ke karkashin ma’aikatarsa.
Dubban mutane a sassan kasar nan ne suka hallara don neman aikin da bai kai na mutum dubu biyar ba a ranar Asabar da ta gabata.
Moro ya shaida wa gidan rediyon BBC cewa akwai ‘sakaci ‘ daga jami’an da suka kula da daukar ma’aikatan, amma ya ce su ma masu neman aikin kamata ya yi su ksance masu hakuri.
Ya ce murabus dina “bai taso ba,” sai bayan bincike.
Ministan ya zargi wasu da hawa ta katangar filin wasa na kasa da ke Abuja inda ake gwaji ga masu neman aiki, lamarin da ya ce shi ya jawo turmutsitsin. Irin wannan kalami nasa a karshen mako ya jawo aka rika kiran ya yi murabus daga mukaminsa.
Ya ce duk da ya dauki alhakin faruwar lamarin saboda kofa daya kawai aka bude a filin wasan amma ba zai sauka ba.
Majalisar Dokoki ta kasa ta bi sahun kungiyar kwadago ta kasa da ta dalibai da kungiyoyin kare hakkin dan Adam wajen kiran a sauke ministan kan faruwar lamarin wanda ya ci rayukan mutum 19 a sassn kasar nan ciki har da mace mai juna biyu.