✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tushen zunubi da hanyar ceto (4)

A cikin bincikenmu na wannan mako, za mu ga me Littafi Mai tsarki ke fadi game da hanyar samun ceto daga zunubi. Kamar yadda muka ji…

A cikin bincikenmu na wannan mako, za mu ga me Littafi Mai tsarki ke fadi game da hanyar samun ceto daga zunubi.

Kamar yadda muka ji a cikin bincikenmu a makon jiya; Yesu ya zo duniya don fansar mu ’yan Adam ta wurin nuna mana hanyar zuwa wurin Uba; Yahaya 14:6 Yesu ya ce masa, “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai ta wurina.”

A duk lokacin da muka karbi Yesu Almasihu ya zama mai cetonmu, Ruhu Mai tsarki zai kasance tare da mu, ya kuma jagorance mu cikin tafarkin Ubangiji.

Na farko, a lokacin da Yesu Almasihu na tare da almajiransa, ya fadakar da su cewa, bayan ya koma wurin Uban, zai aiko musu da mai taimako, domin jagora, wato Ruhu Mai tsarki; cikin Littafin Yahaya 16:5-15, “Yanzu kuwa za ni wurin wanda Ya aiko ni, duk da haka a cikinku, ba wanda ya tambaye ni, ‘Ina za ka?’ Amma saboda na fada muku wadannan abubuwa, ga shi bakin ciki ya cika zuciyarku. Duk da haka ina gaya muku gaskiya, zai fiye muku in tafi, domin in ban tafi ba, Mai taimakon nan ba zai zo gare ku ba. In kuwa na tafi, zan aiko shi gare ku. Sa’ar da kuwa ya zo zai kada duniya a kan zunubi da adalci da kuma hukunci. Wato, a kan zunubi, domin ba su gaskata da ni ba, a kan adalci kuwa, don za ni wurin Uba, ba kuwa za ku kara ganina ba, a kan hukunci kuma, domin an yanke wa mai mulkin duniyar nan hukunci.

“Ina da sauran abubuwa da yawa da zan gaya muku tukuna, amma ba za ku iya daukarsu a yanzu ba. Sa’ar da kuwa Ruhu na gaskiya ya zo, zai bishe ku a cikin dukkan gaskiya, domin ba zai yi magana don kansa ba, sai dai duk abin da ya ji, shi zai fada, zai kuma sanar da ku al’amuran da za su auku. Zai daukaka ni, domin zai dauko daga cikin abin da yake nawa ya sanar da ku. Duk abin da Uba yake da shi, nawa ne. Shi ya sa na ce zai dauko daga cikin abin da yake nawa ya sanar da ku.”

Ya kuma sake fadakar da su a kan Ruhu Mai tsarki idan muka ci gaba da karatu a cikin Littafin Yahaya 14: 16-17: “Ni ma zan roki Uba, zai kuwa ba ku wani Mai taimako ya kasance tare da ku har abada. Shi ne Ruhu na gaskiya, wanda duniya ba ta iya samunsa, domin ba ta ganinsa, ba ta kuma san shi ba. Ku kam, kun san shi, domin yana zaune tare da ku, zai kuma kasance a zuciyarku.” 1 Korantiyawa 6:19-20, “Ashe, ba ku sani ba, jikinku Haikali ne na Ruhu Mai tsarki wanda yake a zuciyarku, wanda kuka kuma samu a gun Allah? Ai, ku ba mallakar kanku ba ne. Sayenku aka yi da tamani. To, sai ku daukaka Allah da jikinku.”

Na biye, Ayyukan Manzanni 2:38: “Sai Bitrus ya ce musu, “Sai ku tuba, a yi wa kowanenku baftisma, a kan kun yarda da sunan Yesu Almasihu, domin a gafarta zunubanku, za ku kuwa samu baiwar Ruhu Mai tsarki.

Na karshe, Manzo Bulus ya yi magana a kan sabo da tsohon mutum a cikin Littafin Romawa 6:1-7: “To, me kuma za mu ce? Ma ci gaba da yin zunubi ne domin alherin Allah ya habaka? A’a, ko kusa! Mu da muka mutu ga zunubi, kaka za mu kara rayuwa a cikinsa har yanzu? Ashe, ba ku sani ba duk daukacinmu da aka yi wa baftisma a cikin Almasihu Yesu, a cikin mutuwarsa aka yi mana baftismar ba? Saboda haka, an binne mu da shi ke nan, ta wurin baftisma cikin mutuwarsa, domin kamar yadda aka tada Almasihu daga matattu ta wurin daukakar Uba, haka mu ma mu yi zaman sabuwar rayuwa.”

Tunda yake mun zama daya da shi wajen kwatancin mutuwarsa, ashe kuwa, za mu zama daya ma a wajen tashinsa. Wato, mun sani an gicciye halayenmu na da tare da shi, domin a hallakar da ikon nan namu mai zunnubi, kada mu kara bauta wa zunubi. Wanda ya yi irin wannan mutuwa kuwa, an kubutar da shi daga zunubi ke nan.

A cikin Littafin Afisawa 4:22-24: “Ku yar da halinku na da, wanda da kuke a ciki, wanda yake lalacewa saboda sha’awoyinsa na yaudara, ku kuma sabunta ra’ayin hankalinku, ku dauki sabon halin nan da aka halitta bisa ga kamannin Allah da hakikanin adalci da tsarki.”

Haka kuma a cikin Littafin Kolosiyawa 2:11-13: “A cikinsa ne kuma aka yi muku kaciya, ba kuwa yin mutum ba, amma wadda Almasihu ya yi muku ce, ta wurin tube halinku na mutuntaka. An kuma binne ku tare da shi a wajen baftisma, inda kuma aka tashe ku tare da shi saboda ban-gaskiyarku ga ikon Allah, wanda Ya tashe shi daga matattu. Ku kuma da kuke matattu saboda laifuffukanku, marasa kaciya ta jiki, Allah Ya raya ku tare da Almasihu, Ya yafe mana dukkan laifuffukanmu.”

Ka karbi Yesu Almasihu yau domin ka samu ceto daga rayuwar zunubi da za ta kai mutum ga hallaka.

Bari Ubangiji Allah Ya albarkace mu, amin.