Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Tuzurai za su rika biyan harajin rashin yin aure a Afirka ta Kudu

Al’umma a kasar Afirka ta Kudu, musamman tuzurai da suka haura shekara 18 a duniya, amma ba su yi aure ba sun shiga rudani, bayan sun samu labarin cewa za su fara biyan haraji saboda ba su da aure.

An nuna cewa, samarin yankin Nkuthu na Arewacin KwaZulu-Natal, za su rika biyan harajin da aka sa wa suna harajin ‘samari marasa aure’ inda duk saurayin da ya haura shekara 18 ba tare da ya yi aure ba, zai rika biya haraji duk shekara, kamar yadda kafar labarai ta News 24 ta ruwaito.

ADVERTISEMENT

Tashar eNCA, ta zanta da wani saurayi mai suna Thamsanka Zwande mai shekara 31, wanda bai da aure, kuma yana zaune ne a kauyen Bulamehlo na yankin Nkuthun da aka sanya dokar, inda ya ce har yanzu bai da aikin yi, don haka sai dai mahaifiyarsa ta biya masa harajin.

A rahoton da News 24 da kalato daga eNCA, duk saurayin da ya haura shekara 18, an aika masa takardar fara biyan kudin haraji duk shekara.

ADVERTISEMENT

Zwande ya nuna cewa, “Eh, lallai an aiko min da takardar. Ba ni da mace ko budurwa da take zama da ni. Don haka zan rika biyan Randi 50 duk shekara.”

Rahoton ya kara da cewa wannan haraji zai shafi iyaye, domin duk wanda yake da dan da ya kai biyan harajin amma bai da aikin yi da zai biya wa kansa, dole nauyin biyan ya koma kan iyayensa.

Wani mai suna Busisiwe Mthembu, wanda yake da ’ya’ya samari guda uku da za su rika biyan harajin, ya shaida wa eNCA cewa, “Dole za su biya wannan harajin duk da cewa ba su da aikin yi. Na biya wa dana na farko, yanzu sauran biyu ma za su kai shekara 18 kwanan nan, dole in karbo musu takardar harajin.

Da yake jawabi game da zargin tursasa mutane da biyan kudi, basaraken yankin da ake kira iNkosi a kabilar Zulu, Thathezakhe Ngobese ya musanta zargin, inda ya ce kawai suna karbar kudi ne domin su yi amfani da shi wajen kula da masarautar da ma’aikatanta, “Amma ba iyalan Ngobese ake tara wa kudin ba,” inji shi.

Ba a Afirka ta Kudu aka fara sanya irin wannan dokar ba, tarihi ya nuna cewa an taba sanya irin wannan dokar a birnin Rum a shekara ta 9 Miladiyyar Annabi Isa, inda basaraken lokacin mai suna Agustus ya sanya doka mai suna “Led Papia Poppaea” domin ya kwadaitar da matasa su yi aure.

Haka kuma a Jihar Missouri ta Amurka, an taba sanya dokar biyan harajin Dala Amurka 1 a kan duk saurayin da bai da aure.