✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

TY danjuma ya cancanci Jamarai Zazzau

Maimartaba Shehu Idris ya tabbatar wa da Janar Yakubu T. danjuma Sarautar Jarmai Zazzau. Hakkika wannan sarauta ta JARMAI ZAZZAU da aka bai wa danjuma,…

Janar T.Y DanjumaMaimartaba Shehu Idris ya tabbatar wa da Janar Yakubu T. danjuma Sarautar Jarmai Zazzau. Hakkika wannan sarauta ta JARMAI ZAZZAU da aka bai wa danjuma, duk da cewa ba ni da masaniyar amfaninta a masarautar Zazzau, amma ko shakka babu Maimartaba Sarki ya bayar da wannan sarauta ga mutumin da ya dace. Lallai Arewa tana da zakakuran ’ya’ya wadanda suka hidimta mata, kuma suka sadaukar da rayuwarsu, don ganin ci gaban yankin Arewa, irin wadannan mutane ba laifi ba ne idan an saka musu da irin wadannan sarautu.
Malam Yakubu T. danjuma, daya ne daga cikin zakakuran ’yan Arewa na tun farko, wadanda duniya ta shaida aikinsu. Hakika mutum irin danjuma idan ba’a yabe shi ba to shakka babu idan aka zage shi akan Arewa, an zalunce shi. Da yawan mutunen Arewa, musamman matasa da suke da karancin sanin me ya faru a baya, kusan tun zamanin su marigayi Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto, an ba su gurbataccen tarihin waye danjuma, domin nakan ji masu san su soki danjuma, sukan ce shi din makiyin Musulunci ne da Musulmi. Wannan kusan ita ce maganar da take fitowa daga bakunan masu san sukar danjuma ko kuma kushe shi.
Wannan kam abu ne “wadeh” wanda Al-kur’ani ya tabbatar kuma dukkan Musulmi ya yi Imani da haka. Amma kuma, Allah cikin nufinsa da kaddarawarsa ya hada Musulmi da wanda ba musulmi ba zama waje guda, don haka ya zama dole dukkan bangarori su san yadda za su zauna da juna lafiya, “ladarara wala dirara” babu cuta babu cutarwa. Allah masani!
danjuma kusan dukkan mutanen da ake kira dattijan Arewa, babu wani mutum sama da shi, idan ban da sa’o’insa irinsu Malam Adamu Chiroma. Tun zamanin Marigayi Sardauna danjuma ya nuna kwazo da kishin Arewa, ina zaton wannan shi ne dalilin da ya sanya Sardauna a wancan lokaci ya ja mutane irinsu danjuma a jiki, dan ya nunawa al’ummar Arewa musamman Musulmi muhimmancin tafiya da mutanan da suke ba Musulmi ba, wajen ciyar da yankin Arewa gaba. Idan za’a yi magana ta gaskiya, kuma za a yi adalci. Dole ne mutanan Arewa su yabawa danjuma, domin shine kadai Mutumin da ya sadaukar da rayuwarsa a lokacin da aka kashe Sardauna, duk masu ihu da karadin Arewa, da cika duniya da surutu, watakila lokacin da danjuma yayi wannan kasadar wa rayuwarsa dan ankashe Sardauna su suna zanin goyo, ko   ma zo duniyar ba. Ba su san lokacin da danjuma ya yi wannan kasadar ba. An ce danjuma Igwa ya dauka zai tunkari mutanan kudancin kasarnan akan kashe Sardauna da aka yi. Allah shi ne masani!
Haka kuma, duk da irin gurbataccen tarihin da ake bai wa ‘yan Arewa akan danjuma, a cikin manyan sojojin da suka rike manyan mukamai da ‘yan siyasa da wahala ka samu wanda ya taimaka wa talakawa da dukiyarsa irin danjuma (Bance babu ba). danjuma bai rike mukamin shugaban kasa ko mataimakinsa ba, amma ya rike mukamin munista, kuma daya ne daga cikin mutanen da Allah Ya yi wa arziki a yankin Arewa, abin da mutane da yawa ba su sani ba, danjuma kusan gaba daya dukiyarsa Musulmi ‘yan Arewa sune suke alkinta masa. Na tabbata mutane suna sane da irinsu Alhaji Amadu Chanchangi na Kaduna, da irin taimakon da ya yi wa al’umma da Musulunci, sanin kowa ne cewar Chanchangi babban na hannun dama ne ga danjuma, wanda kusan dukiyar da Amadu yake tafiyarwa ta danjuma ce gaba daya. Shin idan da danjuma makiyin Arewa ne zai yarda ya danka amanar dukiyarsa a hannun irinsu Amadu Chanchangi?
Watakila wasu su ce ai danjuma ya taimakawa da kungiyar CAN da makudan kudi. Anan sai na ce danjuma ya taimaka wa abin da ya yi Imani da shi ne da kuma addinin sa, a kuma wannan gaba ce za mu kalubalanci dukkan manyan da Najeriya ta yi musu wando da riga dalilin Arewa suka kudance suka yi arziki dare daya, su me suka yi wa talakawan Arewa? Kowa yasan da cewa mutanen da suka rike manyan mukamai irin su IBB da Abacha da AbdusSalam masu arzikin gaske ne, amma tsakaninmu da Allah wace Gidauniya suka kafa domin taimaka wa talakawa da dimbin dukiyar da suka samu? Bar ta batun taimako, shin zakkar da Allah ya umarci dukkan Musulmi su bayar suna bayarwa kuwa?  Bari  mu buga misalin irin dimbin arzikin da mutanen nan suka mallaka. IBB shi ne shugaban kasar Najeriya na soja, wanda ya yi tasarrufi da riyojin man kasar nan yadda yaga dama, a wannan lokacin ne ya bai wa danjuma kyautar rijiyar Manfetur ladar ganin ido. Ka ji masu abin!
Wannan rijiyar manfetur da aka bai wa danjuma kyauta ce, bayan ya kwashe tsawon lokaci yana amfanarta, sannan ya sayarwa da wani kamfanin kasar Koriya da wannan rijiya akan kudi Naira Biliyan Dubu, tashin hankali! Wadannan kudi da danjuma ya samu, ya kafa Gidauniyar TY danjuma, inda ya ware mata Naira Biliyan 15 domin kawai a taimaka wa talakawa da marasa galihu da masu karamin karfi. Wannan kadan ne daga cikin misalin irin yadda danjuma ya yi tasarrufi da dukiyarsa.
Mu koma  kan  IBB, tunda shi ne muntahar, don Allah mai karatu a tunaninka IBB rijiya nawa zai bai wa kansa da iyalansa? Nawa kake zaton ya mallaka? Idan har mutum irin danjuma an bashi rijiya daya ladan ganin Ido ya sayar da ita Naira Biliyan Dubu? Ba wannan ba ma, a lokacin IBB ne fa Gwamnatin Najeriya karkashin jagorancinsa, za ta tono danyen manfetur ta sayarwa da Matatun manfetur na IBB da yake da su a Kwadebuwa da Binin sannan ya tace, ya dawo da tataccen ya sayarwa da gwamnati. Tirkashi, kaji mutum da kasar ubansa!
Kamar yadda bayanai suka nuna cewar danjuma ya taimaka wa CAN da kudi cikin waccan Biliyan Dubun don gudanar da ayyukanta. Don Allah kungiyar IZALA da IBB yake jingina kansa gareta Biliyan Nawa ya taba bata domin ayyukanta? Ko kuma kungiyar Jama’atu Nasrul Islam JNI nawa ya taba ba su? Wace irin gidauniya IBB ya kafa don taimakon Musulmi da Talakawa da ya fito daga cikinsu? Wannan IBB ke nan fa kadai, ina ga irin dukiyar su Abacha da AbdusSalami da Aliyu Gusau da sauran manyan sojoji da suka kwashi dukiyar Najeriya kamar ta ubansu? Amma saboda son KAI da rashin fahimtar yadda gaskiyar lamura suke, sai mu kyale su IBB suna watayawarsu da dukiyarmu da suka kwashe, muna zagin su danjuma. Allah ya kyauta!