Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

TY Danjuma ya yaba wa ‘yan siyasar Jihar Nasarawa

Tsohon Ministan tsaro kuma Shugaban Kwamitin Shugaban Kasa kan Farfado da Arewa maso Gabas, Theophilus Yakubu Danjuma ya yaba wa matakin da wasu jiga-jigan ‘yan siyasa Kiristoci daga jam’iyyun siyasa daban-daban musamman PDP da APC a Jihar Nasarawa suka dauka na don fahimtar juna a tsakaninsu a farkon wannan makon.

Theophilus Danjuma wanda shi ne shugaban taron, ya ce taron shi ne irinsa na farko da aka gudanar a jihohin kasar nan. Ya ce ba shakka hakan ya nuna karara cewa ‘yan siyasa kiristoci a Jihar Nasarawa sun san abin da suke yi, idan aka yi la’akari da bambance-bambancen siyasa dake tsakaninsu, suka ga ya dace su gudanar da taron don su fahimci junansu da hakan a cewarsa zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya tsakaninsu da ma sauran ‘yan siyasa daga sauran addinai a jihar.

ADVERTISEMENT

Danjuma ya kuma bukaci sauran ‘yan siyasa kiristoci su yi koyi da abin da wadannan ‘yan siyasa kiristoci a jihar suka yi, don tabbatar da zaman lafiya da kauna tsakaninsu baki daya. Ya kuma bukaci sabbin shugabannin kungiyar kiristoci a jihar da su tabbatar sun gudanar da harkokin kungiyar cikin gaskiya da rikon amana don tabbatar da dorewar cigaba da ake samu a jihar musamman na hadin kawunan al’ummar kiristoci da ma wadanda ba kiristoci ba a Nasarawa.

Shi ma a jawabinsa Mataimakin Gwamnan Jihar, Mista Silas Ali Agara wanda ya sha kaye a zaben fid da gwani na gwamna a APC a jihar, ya bayyana cewa jiga-jigan ‘yan siyasa kiristocin da sauran kiristoci masu ruwa da tsaki a siyasar jihar sun ga dacewar su shirya taron don tunatar da junansu cewa kodayake kowannensu na da nasa ra’ayin siyasa, amma kada su manta cewa dukkansu daya ne a gun Isah Almasihu.

ADVERTISEMENT

Shi ma a nasa bangaren sabon shugaban kungiyar kiristocin jihar da aka rantsar a yayin taron, Bishop Joseph Masin ya yaba wa hangen nesan da a cewarsa ‘yan siyasa kiristoci daga dukkan jam’iyyu a jihar suka yi, inda ya shawarce su da su kafa wata kungiya ta Kiristoci ‘yan siyasa a jihar da kasa baki daya don kara inganta wannan zumunci da fahimtar juna a tsakaninsu.