Search
Subscribe
U-20: Senegal ta fitar da Najeriya

U-20: Senegal ta fitar da Najeriya

A ci gaba da fafatawa a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya bangaren maza da yanzu haka yake gudana a Katar, a ranar Litinin da ta wuce ne Senegal ta doke Najeriya da ci 2-1 da hakan ya sa ta haye matakin kusa da na karshe wato Kwata-Fainal yayin da Najeriya kuma ta yi ban kwana da gasar.

Najeriya dai ta fafata ne a rukunin D da kasashen Katar da Amurka da kuma Ukraine.

A wasan farko Najeriya ce ta lallasa Katar da ci 4-0 sai wasa na biyu Amurka ta lallasa Najeriya da ci 2-0 sai a wasa na uku Najeriya ta yi kunnen doki da Ukraine da ci 1-1 sai kuma Senegal ta lallasa Najeriya da ci 2-1 a wasa zagaye na biyu.

Jama’a da dama ba su ji dadin yadda kungiyar Flying Eagle ta taka rawa a gasar ba.

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin