✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ubangiji Mai taimakonmu

“Ka gabatar da wahalarka ga Ubangiji, zai kuwa taimake ka, ba zai bari a ci nasara a kan mutumin kirki ba, faufau.”  Zabura 55:22. Godiya…

“Ka gabatar da wahalarka ga Ubangiji, zai kuwa taimake ka, ba zai bari a ci nasara a kan mutumin kirki ba, faufau.”  Zabura 55:22.

Godiya ta tabbata ga Ubangiji Allah Mai taimako, Mai alheri, Mai jinkai. KaunarSa zuwa gare mu ba ta da iyaka. Barkanmu da sake saduwa cikin wannan makon inda za mu ga wasu ayoyi daga cikin Littafi Mai tsarki don karfafawa a duk lokacin da muke neman taimako daga wurin Ubangiji.

Gama a rubuce yake, maganar Ubangiji na da iko, abin da ya kamata mu fahimta a nan shi ne “Ban-gaskiya,” mu zama masu bada gaskiya ga Ubangiji, Shi kuwa ba zai yashe mu ba, domin ban-gaskiyarmu ga Ubangiji za ta ’yantar da mu. Dalilin da mutane ke fuskantar matsaloli da dama har su ga kamar babu hanyar mafaka ko mai taimako shi ne ba su gaskata ikon Ubangiji ba, sun fi dogara ga ikon kansu da kuma abin da mutum zai fada musu. Abin da ya kamata mu sani shi ne, Ubangiji Yana da iko, zai kuma taimake mu a duk lokacin da muke ciki ko muka fuskanci wata matsala.

Ga wasu ayoyi daga Littafi Mai tsarki da za su taimake mu a duk lokacin da muke neman taimako daga wurin Ubangiji, idan muka yi addu’a da ban gaskiya ga Ubangiji.

 

Filibiyawa 4:6-7

“Kada ku damu da komai, sai dai a kowane hali ku sanar da Allah bukatunku, ta wurin yin addu’a da roko, tare da gode wa Allah. Ta haka salamar Allah, wadda ta fi gaban dukkan fahimta, za ta tsayar da zukatanku da tunaninku ga Almasihu Yesu.”

 

1 Yahaya 5:14-15

“Wannan ita ce amincewarmu a gabansa, wato, in mun roki komai bisa ga nufinSa, sai Ya saurare mu. 15 In kuwa muka san komai muka roka yana sauraronmu, mun tabbata mun samu abin da muka roka a gare Shi ke nan.”

 

Matiyu 7:7

“Ku yi ta roko, za a ba ku. Ku yi ta nema, za ku samu. Ku yi ta kwankwasawa, za a kuwa bude muku.”

 

Zabura 46: 1-3

“Allah ne mafakarmu da karfinmu, kullum a shirye yake Ya yi taimako a lokacin wahala. Saboda haka ba za mu ji tsoro ba, ko da duniya za ta girgiza, duwatsu kuma su fada cikin zuzzurfan teku, ko da a ce tekuna za su yi ruri su tumbatsa, tuddai kuma su girgiza saboda tangadin tekun.”

 

Romawa 10:10-13

“Domin da zuci mutum yake gaskatawa ya samu adalcin Allah, da baki yake shaidawa ya samu ceto. Gama nassi ya ce, “Duk mai gaskatawa da Shi ba zai kunyata ba.” Ai, ba wani bambanci a tsakanin Bayahude da Ba’al’umme. Ubangijin nan daya Shi ne Ubangijin kowa, Mayalwacin baiwa ne kuma ga dukkan masu addu’a a gare Shi. Duk wanda kuwa ya yi addu’a da sunan Ubangiji zai sami ceto.”

 

Ibraniyawa 13:5-6

“Kada halinku ya zama na son kudi. Ku dangana da abin da kuke da shi, gama Allah kanSa Ya ce, “Har abada ba zan bar ka ba. Har abada kuma ba zan yashe ka ba.” Saboda haka, ma iya fitowa gaba-gadi, mu ce, “Ubangiji Shi ne Mataimakina,  ji tsoro ba. Me mutum zai iya yi mini?”

 

Zabura 107:28-30

“Cikin wahalarsu suka yi kira ga Ubangiji, Ya kuwa cece su daga azabarsu. Ya sa hadari ya yi tsit, Rakuman ruwa kuma suka yi shiru. Suka yi murna saboda wurin ya yi shiru, Ya kuma kai su kwatar jiragen ruwa lafiya, Wurin da suke so.”

 

Zabura 124:8, 125:1

Taimakonmu daga wurin Ubangiji yake zuwa, Shi Wanda Ya yi sama da duniya.

Wadanda suke dogara ga Ubangiji, Suna kama da Dutsen Sihiyona, Wanda ba zai jijjigu ba, faufau. Faufau kuma ba za a kawar da shi ba.”

 

Zabura 119:169-176

“Bari kukana ya kai gare Ka, ya Ubangiji! Ka ganar da ni kamar yadda Ka alkawarta. Bari addu’ata ta zo gare Ka, Ka cece ni kamar yadda Ka alkawarta. Zan yabe Ka kullum, Domin Ka koya mini ka’idojinKa. Zan rera waka a kan alkawarinka, Domin umarninka a gaskiya ne. Kullum a shirye Kake domin Ka taimake ni, Saboda ina bin umarninKa. Ina sa zuciya ga cetonKa kwarai, ya Ubangiji! Ina samun farin ciki ga dokarKa. Ka rayar da ni don in yabe Ka, Ka sa koyarwarKa su taimake ni! Ina kai-da-kawowa kamar ɓatacciyar tunkiya, Ka zo Ka neme ni, ni bawanKa, Saboda ban ki kulawa da dokokinKa ba.”

 

Zabura 46: 1-3

“Allah ne Mafakarmu da karfinmu, kullum a shirye Yake Ya yi taimako a lokacin wahala. Saboda haka ba za mu ji tsoro ba, ko da duniya za ta girgiza, duwatsu kuma su fada cikin zuzzurfan teku, ko da a ce tekuna za su yi ruri su tumbatsa, tuddai kuma su girgiza saboda tangadin tekun.”

 

Zabura 146:5-10

“Mai farin ciki ne mutumin da Allah na Yakubu ne Yake taimakonsa, Yana kuma dogara ga Ubangiji Allahnsa, wanda Ya halicci sama da duniya da teku, Da dukkan abin da yake cikinsu. Kullum Yakan cika alkawarinSa. A yanke shari’arsa takan ba wanda aka zalunta gaskiya. Yana ba da abinci ga mayunwata. Ubangiji Yakan kuɓutar da daurarru. Yakan ba makafi ganin gari. Yakan daukaka wadanda aka wulakanta. Yana kaunar jama’arSa, adalai. Yakan kiyaye baki wadanda suke zaune a kasar. Yakan taimaki gwauraye, wato matan da mazansu suka mutu da marayu. Yakan lalatar da dabarun mugaye. Ubangiji Sarki ne har abada! Ya Sihiyona, Allahnki zai yi mulki har dukkan zamuna! Yabo ya tabbata ga Ubangiji!”

Shalom.