✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

UEFA ta ci tarar Cristiano Ronaldo kan murnar cin kwallo

Hukumar Kwallon Kafa ta Turai (UEFA) ta ci tarar dan wasan gaba na Jubentus, Cristiano Ronaldo saboda murnar da ya yi lokacin da ya zura…

Hukumar Kwallon Kafa ta Turai (UEFA) ta ci tarar dan wasan gaba na Jubentus, Cristiano Ronaldo saboda murnar da ya yi lokacin da ya zura kwallaye a wasansu da kungiyar Atletico Madrid a gasar Zakarun Turai.

Ronaldo mai shekara 34, ya kwaikwayi yadda kocin Atletico Madrid wato Diego Simeone, ya yi tasa murnar a fafatawar farko da Atletico Madrid ta doke Jubentus 2-0 a Spain. Dan wasan ya juya cikin ’yan kallo da kafafuwansa bude yana ihu domin murnar kwallo ta uku da ya jefa a ragar Atletico a karawa ta biyu a Italiya.

Kwallaye uku rigis da Ronaldo ya ci ne suka taimaka wa Jubentus nasarar tsallakawa zagayen wasan daf da na kusa da na karshe kamar yadda BBC ya ruwaito.

Shi ma kocin Atletico Madrid an ci tararsa Fam dubu 17, wanda ya yi daidai da Naira miliyan 8 saboda murnar da ya yi a wasan na farko.

Jubentus a wasa na gaba an hada ta wasa da Ajad ta Holland bayan ita ma ta yi waje da Real Madrid wadda ta lashe kofin sau uku a jere.