✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ukraine ta lalata wa Rasha makamai masu linzami biyar

Zelensky na ci gaba da neman abokansa na Turai da su ba shi makamai masu cin dogon zango.

 

Rundunar Sojojin Saman Ukraine ta ce ta lalata makamai masu linzami guda biyar da Rasha ta yi amfani da su wajen kai hari a yankunan Kharkiv da Zaporizhia.

Ukraine dai ta bayyana cewa ta fuskanci wannan sabon harin makami mai linzami da jiragen sama marasa matuka daga Rasha.

Sai dai rundunar sojojin saman Ukraine ta ce ta lalata makamai masu linzami na Rasha guda biyar a yankunan da ke Gabashin kasar.

DW ya ruwaito cewa ba a dai bayar da rahoton asarar rai ba a wannan harin, sai dai cibiyoyin makashi da dama sun lalace.

Tun a watan Oktoban da ya gabata ne Fadar Mulki ta Moscow ta rubanya hare-hare a wurare masu mahimmanci na Ukraine, lamarin da ke jefa miliyoyin ’yan kasar cikin tsananin duhu da sanyi na tsakiyar hunturu.

Sabon harin na zuwa ne bayan wani rangadin da Shugaban Kasar Volodymyr Zelensky ya kai Turai don neman karin makamai daga kawayenta.

Shugaba Volodymyr Zelensky na ci gaba da neman abokansa na Turai da su ba shi makamai masu cin dogon zango da jiragen yaki don samun damar tinkarar kasar Rasha.