✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Umaru Dikko ya amince ya shugabanci kwamitin ladabtarwar PDP

Tsohon Ministan Sufuri a Jamhuriya ta Biyu Alhaji Umaru Dikko ya tabbatar a shirye yake ya shugabanci Kwamitin Ladabtarwa na Jam’iyyar PDP. A watan Yuli ne…

Alhaji Umaru DikkoTsohon Ministan Sufuri a Jamhuriya ta Biyu Alhaji Umaru Dikko ya tabbatar a shirye yake ya shugabanci Kwamitin Ladabtarwa na Jam’iyyar PDP.
 A watan Yuli ne Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar PDP na kasa ya kafa kwamitin amma aka kasa kaddamar da shi sakamakon jinyar da aka ce Umaru Dikko ya fita kasar waje.
Sakataren Dikko Alhaji Shehu Sulaiman ya shaida wa wakilinmu a ranar Talata cewa tsohon ministan zai halarci kaddamar da kwamitin da kansa a yau Juma’a. Sulaiman ya ce Alhaji Umar Dikko ya dawo kasar nan a Lahadin makon jiya, kuma ya samu sauki sosai, “zai halarci kaddamar da kwamitin a Abuja,” inji shi.
Lokacin da shugabannin jam’iyyar ta kasa suka ba da sanarwar kafa kwamitin Alhaji Umaru Dikko yana jinya a kasar waje, wanda haka ya jawo tsaiko wajen kaddamar da kwamitin.
Kuma a lokacin da aka bayyana sunan Alhaji Umaru Dikko a matsayin shugaban kwamitin an rika nuna shakku kan kasancewarsa dan jam’iyyar . Sai dai bayanai sun nuna cewa ya koma PDP  a baya-bayan nan.