✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

UNICEF ta yi Allah wadai game da amfani da yara wajen kai hari

Asusun kula da yara kanana na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya yi Allah wadai game da amfani da yara wajen kai hare-haren kunar bakin wake…

Asusun kula da yara kanana na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya yi Allah wadai game da amfani da yara wajen kai hare-haren kunar bakin wake don tada bamabamai a duk yankunan Najeriya musamman yankunan Arewa maso Gabas.

Wakilin UNICEF ana Najeriya Peter Hawkins, ya bukaci duk wadanda suke da hannu a rikicin da su kare yara daga hare-haren da ake kaiwa a kowane lokaci don tsare su daga hadarin harin.

Peter Hawkins, ya ce a harin da aka ranar Lahadi a garin Konduga jihar Borno wanda ya yi sanadiyyar kashe mutum 30 da raunata sama da mutum 40, yara uku ne suka kai harin kunar bakin waken, cikin su akwai mata biyu da namiji daya.