Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

United ta fara zawarcin Dybala

Rahoton da ke fitowa daga kulob din Manchester United na Ingila ya nuna mahukunta kulob din sun fara zawarcin dan kwallon Jubentus na Italiya Paulo Dybala.

Kulob din Jubentus dai ya dora farashin Fam miliyan 85 (kimanin Naira biliyan 40 da miliyan 350) ga duk mai bukatar sayen dan kwallon.

ADVERTISEMENT

Yanzu haka Dybala yana hutu a Ingila kuma da wuya ya sabunta kwantaraginsa a kulob din Jubentus wanda hakan ya ba United damar yin zawarcinsa. Idan United ta sayi Dybala hakan zai ba ta damar sayar da dan kwallon gabanta Romelu Lukaku.

Kocin United, Ole Gunnar Solksjaer ya bayyana aniyarsa ta yin garambawul a kulob din United kafin a fara kakar wasa mai zuwa.

ADVERTISEMENT

Wadansu daga cikin ’yan kwallon United da ake ganin za su bar kulob din sun hada da Paul Pogba da Romelu Lukaku da Anthony Martial da Aledis Sanchez da Antonio Balencia da sauransu.