Notice: Undefined index: show_thumbnails in /var/www/html/am20pow/wp-content/plugins/jetpack/modules/related-posts/jetpack-related-posts.php on line 199

Notice: Undefined index: show_headline in /var/www/html/am20pow/wp-content/plugins/jetpack/modules/related-posts/jetpack-related-posts.php on line 200
United ta shiga zawarcin Mandzukic da Dembele - Aminiya
Aminiya

United ta shiga zawarcin Mandzukic da Dembele

Ole Gunnar Solskjaer

Kocin Manchester United na Ingila Ole Gunnar Soljksjear ya ce shirye-shirye sun yi nisa wajen sayo ’yan kwallon gaba a watan Janairu mai zuwa idan aka bude kasuwar cinikin ’yan kwallo.

Daga cikin ’yan kwallon da kulob din United zai yi zawarci sun hada da Mario Mandzukic na Jubentus da ke Italiya da kuma Ousmane Dembele na FC Barcelona da ke Spain.

Ya ce tuni ya tattauna batun da mahukunta kulob din United kuma sun amince masa ya fara zawarcin ’yan kwallon da zarar an bude kasuwar ’yan kwallo a watan Janairun badi.

United tana fama da matsalar ’yan kwallon gaba bayan da ta sayar da Romelu Lukaku. Yanzu haka ’yan kwallon gabanta Marcus Rashford da Anthony Martial kumja suna jinyar raunin da suka ji.

ADVERTISEMENT