✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Usaini Mohammed ya zama Ajiyan Sintalin Yeriman Gombe

Alhaji Ibrahim Abubakar Sintalin Yeriman Gombe, kuma Mai Unguwar Kumbiya kumbiya A. Ya Nada Usaini Muhammed dan Yaro matsayin Ajiyan Sintalin Yerima. Alhaji Ibrahim ya…

Alhaji Ibrahim Abubakar Sintalin Yeriman Gombe, kuma Mai Unguwar Kumbiya kumbiya A. Ya Nada Usaini Muhammed dan Yaro matsayin Ajiyan Sintalin Yerima.

Alhaji Ibrahim ya nada Usaini ne wannan sarautar ta Hagalare saboda biyayya da kuma samun mataimaki a fadar Yeriman Gombe don rage masa wasu aikace-aikace.

Da yake jawabi a wajen nadin na Ajiyan nasa a ranar Asabar da ta gabata, Sintalin ya ce biyayya da kuma dacewa tasa ya bai wa Usaini Ajiyan Sintalin tun cikin Azumi, amma sai yanzu aka masa wanka na nadi.

Sintali ya ce ya nada Usaini ne da izinin Yeriman Gombe wanda shi ne babban Hakimin cikin garin Gombe da kewaye, sannan ya godewa Allah na yadda ya ba shi ikon gudanar da wannan nadi a dai dai wannan lokaci.

Ibrahim Abubakar ya kara da cewa ya tabbata Ajiyan sa ba rago bane kuma ba zai ba shi kunya ba, sannan sai ya yi kira ga sauran masu rike da sarautu na hagalare da cewa su hada kai wajen ciyar da masarautar Gombe da ma ita kanta Jihar Gombe gaba.

Da yake zantawa da Aminiya jim kadan bayan nada shi Ajiyan Sintalin Yeriman Gombe, Usaini Muhammed dan Yaro, ya ce gaskiya yana cike da farin cikin da ba zai misaltu ba domin tun a cikin watan azumin da ya gabata ne Sintali ya bashi wannan sarautar a wani lokacin da ya je  gaishe a gida.

Ya ce da ya gayawa mahaifiyarsa cewa Sintalin Yeriman Gombe ya ba shi wannan sarauta sai ta yi masa addu’a da cewa Allah Ya kai mu lokacin da za ayi nadi.

Sabon Ajiyan Sintalin ya yi amfani da wannan damar wajen yin kira ga matasa ‘yan uwansa da cewa su gane biyayya ta na da kyau kuma ta na da rana, inda ya ce biyayyarsa ta sa aka ba shi wannan sarauta har suka taru suke taya shi murna.

Har ila yau ya kuma sake yin amfani da wannan dama wajen godewa mai martaba uban kasa Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar na III da Yeriman Gombe Hakimin cikin gari da kewaye wanda da yardar shi aka nada shi ya zama basarake.

Ya yi alkawarin cewa duk wata hidima da ta taso na mai martaba Yeriman Gombe da shi za ayi saboda shi ma yanzu albarkacin Sintali ya zama dan cikin gida, kuma duk wata gudumawa daidai gwargwado da biyayya zai yi wa fada. Daga nan sai ya godewa Alhaji Ibrahim Abubakar Sintalin Yeriman Gombe bisa wannan sarauta ta Ajiyansa da ya dauko shi cikin dubu ya nada shi.

Sannan sai ya godewa dukkan jama’ar Unguwar Kumbiya kumbiya da Masu unguwanninsu da Dagaci Malam Audu Kafinta da iyayensa da abokan arziki na addu’ar fatar alherin da suka masa. Bayan kammala nadin sarautar Ajiyan Sintalin Yeriman Gombe, abokai sun yi hawan Dawakai don taya Usaini murna.