✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Uwa ta kirkiro wa ’yarta diyar bebi mai karatun kur’ani

Wata uwa ’yar kasuwa a kasar Faransa Samira Amarir ta yi matukar kokarin ganin ta samar da kayan wasa da za su koya wa ’yarta…

Wata uwa ’yar kasuwa a kasar Faransa Samira Amarir ta yi matukar kokarin ganin ta samar da kayan wasa da za su koya wa ’yarta addinin Musulunci, don haka ta kirkiro da ’yartsana mai karatun Alkur’ani. Yan zu diyar Bebin dka aka yi wa lakabi da “Jenna” wadda ta kirkiro tana karanta wasu surori daga Alkur’ani, har ta kai ga an yi irinta da yawa ana sayarwa a kasashen yankin Tekun Pasha.

“Lokacin da ’yata ta kai shekara biyu, sai na fara neman kayan wasa ko wata na’ura da za ta koya mata Alkur’ani,” inji Amarir.

“Manufar dai ita ce a samar da kayan wasa da za su taimaka mata wajen koyon karatun Alkur’ani cikin sauri, a saukake lokacin da take wasa,” Jenna, wadda sunanta ya samo asali daga Aljanna, an sanya mata abaya da dankwali mai launin ruwan goro.

Wajen zayyanar ‘’yar tsanar an yi amfani da masarrafar kwamfuta a shafukan intanet, inda Amarir ta yi mata launin duhu-duhu a fatarta tare da kwalliyar fuska.

“A gareni yana da muhimmanci diyar bebi ta fito da siffar da ’yata za ta iya fahimta, ko ta gane mahaifiyarta,” inji ta.

Surori hudun da Jenna ke karantawa gajeru ne, wanda aka jero yadda yaro zai iya haddacewa. Cikin klwanaki kadan  da fara wasa da ’yar bebi sai ta fara karanta ayoyi.

Amarir da iyalanta sun bar kasar Faransa, inda suka koma kasar Hadaddiyar Daular Larabawa don tallata wannan ’yar bebi. Bayan da ta shafe shekara hudu tana kai-kawo a masana’antun kasar Sin da suka kera ’yar bebi, a farko-farkon wannan shekarar ta kaddamar da Jenna a kasashen Saudiyya da Kuwait da UAE.