Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Uwa ta sayar da jaririnta dan kwana daya kan Naira dubu 500

Uwa ta sayar da jaririnta dan kwana daya kan Naira dubu 500

Rundunar ’Yan sandan Jihar Imo ta kama wata mace da ta sayar da ’yarta jaririya kwana daya a kan kudi Naira dubu 500.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, Orlando Ikeokwu ya shaida wa manema labarai cewa rundunar ta kama matar ce mai suna Chinasa Ukaonu da wadansu mata biyu ma’aikatan asibiti da suka taimaka mata wajen sayar da jaririyar da suka hada da Dorothy Esomonu da Catherine Eke da kuma wadda  ta sayi jaririn mai suna Chioma Amadi wadanda zuwa yanzu Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Alhaji Rabi’u Ladodo ya ba da umarnin a ci gaba da bincike a kan su kafin daga bisani a gurfanar da su domin su fuskanci shari’a.

Kakakin ya ce a ranar 1 ga Agustan nan ne rundunar ta kama wadanda ake zargin bayan koken da mijin matar Mista Promise Ukaonu ya kai ,inda aka samu nasarar kama Chinasa Ukaonu da Chioma Amadi da Esomonu Dorothy da kuma Catherine Eke.

Mijin ya ce matarsa ta fada masa za ta yi tafiya a wancan lokacin. “Bayan binciken da mijin ya yi sai ya gano ba ta  wurin da ta fada masa za ta je, daga bisani sai ta kira shi ta shaida masa cewa dansu ya mutu. Koda ya ce yana so ya ga gawar, sai ta ce ta sanya a leda ta jefar. Lamarin da ya nuna rashin gamsuwarsa a kai kuma ya sanar da ofishin ’yan sanda muka yi bincik muka gano jaririn,” inji shi.