Da Dumi Dumi

Wa ya kamata ya yi wa gawa wanka?

Ba kowa ne yake son jin batun mutuwa ba, wanda haka ya sanya wasu ba su son ma a rika tattauna batunta a kusa da su ko kuma a gare su. Haka ma, hatta wasu mutanen da suka sha daga kogin ilimi kuma suka yi imani da cewa akwai tashin kiyama kuma suke kwadayin shiga Aljanna, amma duk da haka ba su son a rika tattauna batun mutuwa ko al’amarinta. Mafi yawan labarin da aka fi son ji ko yake da dadin ji, shi ne na ganima da ni’imar da ke cikin Aljanna. Haka za ka ga fuskar mutum na annuri, ana murmushi da murna, idan ana labarin Aljanna.
A daya bangaren kuma, da zarar an fara batun mutuwa ko kuma irin matsalolin da ke tattare da ita, nan za ka ga fuskoki suna tsukewa, nan za ka ga mutane na nuna tsoro a fuskokinsu. Haka ma abin yake kasancewa idan mutum ya ji batun irin ukubobi da bala’in da ke cikin kabari, da irin tambayoyin da ake fuskantarwa ga mamaci a cikinsa. Haka ma abin yake kasancewa, idan an zo ga batun ranar hisabi da matsalolin da ke cikinta. Don haka, abin da ya kamata mu sani shi ne, duk yadda za mu tsoraci mutuwa ko kwanciyar kabari, haka kuma duk yadda za mu kaunaci shiga Aljanna, babu yadda za mu shiga Aljanna har sai mun mutu. Ke nan, a batun gaskiya, babu yadda za mu yi, babu yadda muka iya, tun da dai mutuwa ta zama dole.
A wannnan zamani da mutane ke alfahari kuma suke nuna matukar sha’awar kawar rayuwa (kudi, mata, gidaje da sauransu), salihan bayi ne kawai suke hankalta kume suke ankara da cewa, a duk lokacin da aka wayi gari, to kwanukanmu ne suke shudewa, muna kara kusanta da mutuwa. A duk lokacin da hasken safiya ya bayyana, rana ta bullo, ta yi ta tafiya har zuwa faduwa, to lokacinmu ne ke tafiya, muna kara kusantar kabari. A lokacin da haka ke faruwa, shi kuma mummunan makiyinmu, wato Shaidan, yana kara mantar da mu, yana kara shagaltar da mu, domin mu mance da mutuwa, mu mance da kwanciyar kabari. Yakan baibaye mu da shagalce-shagalcen duniya, ta yadda ba mu la’akari da gargadin da lokaci ke bijiro mana da shi. Wadanda suka banzatar da kawunansu a hannun Shaidan, su ne za ka ga sun shagaltu da tsare-tsaren duniya. Haka za ka ga suna ta lissafta burace-buracen duniya, har ma da abin da suke so ya kasance da su a 2015, shekarar da Allah ne kadai Ya san wanda zai kai zuwa gare ta. Ba ita kadai ba, Allah ne kadai Ya san wane ne zai kara minti daya ko awa daya ko kwana daya a rayuwarsa.
Wani al’amari ne ya faru, wanda shi ne ya taso mani da tsimin kawo wannan batu a shafin nan. Wato lokacin da babban yayanmu (wanda muke kira da lakanin kawu, domin ya grime mana da shekaru masu yawa) ya rasu. Bayan ya rasu ne, sai na ce ni zan yi masa wanka kuma in kintsa shi, duk kuwa da cewa wasu sun nuna cewa suna son su yi masa wanka. Nan fa sai wasu mutane da suka zo ta’aziyya suka rika kallo na wani banbarakwai. Ina sane da abin da ke faruwa a irin wannan yanayi a Najeriya, inda, idan wani ya mutu, sai a samu limamin yankin ko wani babban malami, a ce shi zai sallaci gawar; kamar yadda Sunnar Manzo (SAW) ta tanada, ko kuma idan haihuwa ce ko kuma daurin aure, a ce shi zai yi addu’a. Ni kuwa a sani na, idan batu ya zo na yi wa mamaci lufafa, hakki ne na ’yan uwa da magada su yi wa mamacinsu, duk da cewa za su iya gayyato wani ko wasu idan sun ga dama. Dalilin da ya sanya hakkin wankan yake kan ’yan uwa da magada shi ne, saboda akwai wasu sassa na jikin mutum da kawai su ne shari’a ta amince su gani, ba bare ba. Irin wadannan sassan jiki, babu makawa mai yin wankan nan ya gan su, a yayin da yake wankan gawar.
A yayin da aka samu magada ko ’yan uwa na kusa da mamaci suka samu kansu cikin kasawa saboda jimamin rashin dan uwan nasu ko kuma saboda wani dalili mai karfi, babu laifi a gayyato wanda zai iya a madadinsu amma dai ya zama wajibi a yi taka-tsan-tsan, ta yadda dole ne a kula da sirrin mamacin, abin da ya danganci tsiraicinsa. Kuma wankan mamaci ba abu ne da za a yi shi ta hanyar gamgami ba, wato ba za a ce a tara mutane da yawa ba, a ce za a yi wankan gawa.
A lokacin da na shiga dakin da aka ajiye gawar yayan nawa, na sha mamaki da na ga mutane da yawa a ciki. A lokacin da na roki mutane, cewa ya kamata su rage su fita waje, na san cewa mutane da dama sun rika ganin bai kamata ba, suna mamaki. Babu shakka makaruhi ne a shari’a ga mutanen da ba su da dalili da gawar, su ce za su kasance inda ake mata wanka. A yayin yi wa mamaci wanka, ana bukatar magada ne kawai da wadanda suka zama dole gare shi. Kamar yadda malaman addini suka tabbatar, an gindaya wadannan sharudda ne domin a magance matsalar da kan-je-ta-zo, inda wadanda ba ahalin mamaci ba, su je bayan an gama wanka su yi ta surutu kan wani cikas da suka gani a jikin mamacin. Wannan dalili ne ma ya sanya ake zabar mutane masu amana, masu gaskiya da adalci, domin su yi wankan gawa, musamman ma idan ahalin gawar ba su samu damar kasancewa masu yin wankan ba.
Shari’a ta hukunta cewa, maza ne kadai za su wanke maza ’yan uwansu, mata kuma su wanke mata ’yan uwansu. Idan kuwa mace ta mutu a yayin tafiya kuma aka rasa mace a wurin wacce za ta yi mata wanka, kuma aka rasa mijinta ko muharraminta daga cikin mazan da ke wurin, to sai a yi mata taimama kawai. Haka abin yake idan namiji ne abin ya shafa.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya