✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wa ya tsine wa Najeriya? (3)

Shi ya sa daga shekarar 1983 aka fara ganin alamun ’yan Najeriya na cikin tsaka mai wuya. Ba kuma wani abu ya jawo haka ba…

Shi ya sa daga shekarar 1983 aka fara ganin alamun ’yan Najeriya na cikin tsaka mai wuya. Ba kuma wani abu ya jawo haka ba sai ganin Najeriya ta dai tsine wa wasu daga cikin ’ya’yan nata. Saboda haka wahala da damuwa da kunci sun fara zama ruwan dare, duk da cewa an samu wasu da suka nemi su dinka wa Najeriya sabuwar riga ko zane, amma ba a bar su suka kai labari ba, haka al’amurra suka ci gaba da gudana har zuwa 1985. Shi ya sa aka shiga watangaririya da Najeriya, wannan mai karfin hali ya kashe wancan da ya ki goya masa baya. Wannan dakaren daga cikin ’ya’ya ya sa bindiga ya harbe wancan, wancan ya boye a wata kwana yana jira wani ya leko, shi kuma ya buge shi. Haka aka yi ta fama tun daga 1985 har zuwa 1999. Ba rana ko wata da ’ya’yan nan suka taimaka wa Najeriya, in ba cin mutuncinta ba. In ta yi asusu ta tara dukiyar, su bi su sace! In ta matsa su yi ayyukan ci gaba don ciyar da ita gaba, su fara zagi da watsar mata da duk wani tanadi da ta yi domin ’yan baya. Tsinannun ’ya’yan nata ne suka bi duk harkokin da ta tanada na ilimantar da wasu ’ya’yan suka lalata, makarantun da ta tsara domin talakawa da marasa galihu, suka fancakalar da su, suka gina nasu da na ’ya’yansu. Kowa sai tsuwa da ihu. Me zai hana Najeriya ta ci gaba da tsine wa irin wadannan ’ya’yan nata?
Mu tsaya mu yi wa kanmu hisabi. Shin idan Najeriya ba ta tsine wa ’ya’yanta ba ne, me ya sa kullum abin da ke tashe a cikin kasar shi ne wayyo Allah da ni-’ya-su. ’Ya’yanta, musamman shugabanni a kowane mataki sun kasance makafi, ba su gani balle su agaza wajen ciyar da ita gaba. Ba abin da suka gwanance a kai face halin dan bera, abin ban haushin shi ne, in sun sace, ba su san su tsaya su ci da ’yan uwa ba, sai dai su kwashe su je su kimshe a wata kasar don mugunta. Idan ba wadanda aka tsine wa ba, wa ke da wannan dabi’ar?
Mu dubi masu kudi da tarin dukiyar da ke cikin kasar nan, sun tara, sun sake tarawa, wasu daga cikinsu, su ne suka fi kowa tara dukiya a Nahiyar Afirka, amma in ka tambaya wace gudunmawa suka bayar wajen raya gida Najeriya, babu abin a zo a gani. Su ne da manyan-manya da kuma tafka-tafkan gidaje da jiragen sama da shiga dibga-dibgan motoci da banzatar da duk wani abu da zai taimaki jama’a. Duk da tarin dukiyar, amma makwabta da ’yan uwa na kusa da su, na cikin tasku. Shi ya sa kullum suke cikin zullumi da tashin hankali. Idan uwarsu Najeriya ba tsine musu ta yi ba, ina dalilin aukuwar haka?
Wasu daga cikin ’ya’yan nata, wai su ne malamai da fastoci, amma addu’ar da suke faman yi kullum iyakarta a cikin tafin hannunsu. Ba komai ya jawo haka ba, sai ganin bakin da ke furta addu’ar, bai tafiya tare da kyakkyawar zuciya. Shi ya sa suna neman sauki daga Allah, shi kuwa Allah na kara azabtar da su da sauran al’umma, ba wani abu da ya jawo haka ba, sai alamun cewa lallai mahaifiyarsu ta yi musu baki, dole suke lalacewa da balbalcewa.
A kula da kyau, ba wai ’ya’yan Najeriya daga cikin shugabanni da malamai da attajirai kadai abin ya shafa ba, hatta talakawa ba a bar su a baya. Su ne ya kamata a ce ana ganin kamun kai da tausaya wa uwa mai ba da mama. Amma me ke faruwa, su ne ma kan gaba wajen lalacewa. Mai sayar da man gyada a kasuwa ita ce mai gwama man gyadar da kwantarola domin ta samu kazamar riba. Mai daukar kayan mutane a wilbaro a dora masa, kafin mai kaya ya ankara ya bace a cikin duhun jama’a da kayan mutane, don dai ya ji dadin rayuwa. dalibi da ke karatu tun daga firamare har jami’a ba abin da ya fi mayar da hankali irin satar jarabawa, ba don komai ba don ya samu satifiket da zai nemi aikin da zai dage ga yin almundahana da lalata lamurra. Ko’ina ka duba a cikin Najeriya, ba abin da Najeriya ke yi da ’ya’yan nata sai Allah-wadai da sake tsine musu, domin kuwa ba su san Allah ba, ko kuma cewa Annabi ya faku ko kuma akwai wani abu tashin kiyama. Shi ya sa ko’ina ka shiga sai kumaji da share gumin wahalar rayuwa. A kasuwa, ba sauki, an tsula wa kaya kudi domin a samu kazamar riba, mai saye na kuka, wanda aka kasa sayen kayan hannunsa na kuka. Go-sulo a tituna. Lalatattun tituna da godabai. Rashin ruwan sha; na famfo ko makamancin haka. Rashin wutar lantarki, inda ake da wutar lantarkin, idan a ranar ana kwallon kafa a Turai an shiga uku, domin wasu za su je su ba da cin hanci domin a hana jama’a wuta, don mutane su fita kallon kwallo a shagunan da suke da janareto, su biya, su kuma su samu kudi, a-haha. Dukkan wadannan mene ne in ba alamun cewa uwa ta tsine wa ’ya’yanta ba?
Saboda haka idan dai muna son al’amura su canja a cikin kasar nan, to, dole ne mu koma mu nemi uwarmu, mahaifiyarmu Najeriya ta yafe mana laifuffukan da muka yi mata a cikin tsawon rayuwa. Wannan shi ne mafita. Idan Najeriya ba ta sahale mana ba, ta hakura ta yafe mana, to, kuwa mun dai yi ci gaban mai shiga rijiya ke nan. Ba za mu taba ganin haske a gabanmu ba. Tattalin arzikinmu ya rika watangaririya ke nan. Iliminmu da na ’ya’yanmu ya rika shiga tasku ke nan. Siyasarmu ta rika tangal-tangal ke nan. Zamantakewarmu ta rika zubargada ke nan. Shi ya sa ba za mu taba rabuwa da barayi da masu yankar kai da masu madigo da ludu da karuwai da mabarata da cututtukan zamani ba. Shi ya sa talauci da cin hanci da baba-kere da almundahana da zagin juna da rashin zaman lafiya da rashin hadin kai ba za su rabu da mu ba. Shi ya sa komai muke bida daga Allah ba zai ba mu ba, domin bakin mahaifiya na biye da mu. Mafita kurum mu dawo ga Allah, mu kuma nemi Najeriya gafara, idan kuma ta yafe mana, to mu ci gaba da yin aiki tukuru, domin ciyar da kasa gaba! Fakat!
Mun kammala