✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wa za ka aura tsakanin kazama da jahila?

Misali a ce ga ’yan mata guda biyu, an ba ka zabi ka auri guda daya daga cikinsu. Daya kazama ce wacce ba abin da…

Misali a ce ga ’yan mata guda biyu, an ba ka zabi ka auri guda daya daga cikinsu. Daya kazama ce wacce ba abin da ta sani sai kazanta a rayuwarta, daya kuma jahila ce da ba ta da ilimin komai. Wakilanmu sun tattaro ra’ayoyin mutane daban-daban kan wannan batu, kamar haka:

Gara in auri kazama – Augustine

Daga Bashir Liman, Jos

Dung Anthony Augustine, Ma’aikacin Gwamnatin Tarayya: Gara in auri kazama, domin jahilci ya fi hauka ciwo, kuma idan ka auri mace jahila za ta iya zama kazamar ma, saboda ba ta da ilimin komai, abubuwan da dokoki da kuma sharuddan auren ma ba ta sani ba, ba za ka iya jin dadin zaman aure da jahila ba. Duk matar da ba ta san muhimmancin ilimi ba, to ba za ta san muhimmancin aure ba, yadda ba ta damu ta nemi ilimi ba, haka ba za ta damu da rikon aure ba.

Ko da an samu haihuwa jahilar mata ba za ta damu da ilimin ’ya’ya ba, haka su ma ’ya’yan mutum za su taso cikin jahilci, zai zama zaman gidan ma ba zai yi dadi ba, saboda jahilci ma matar za ta iya zama kazama saboda ba ta san muhimmancin tsabta ba.

Na zabi kazama – Adamu Gangariya

Daga Musa Kutama, Kalaba

Adamu Gangariya: Gara in zabi kazama saboda ita kazantarta a iyakanta ta tsaya, ita kuwa jahila har ’ya’yanta abin zai shafa. Zama da jahilar mace abu ne mai matukar wuyar gaske. Da wuya ka iya zama da jahila, ita kuwa kazama akwai hanyoyi da dama da za ka iya bi ka koya mata  tsabta.

Gara in auri jahila – Peter Azi

Daga Bashir Liman, Jos

Peter Azi, dan jarida, mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum a Jihar Filato: Gara in auri jahila, domin soyayyar da take mini za ta iya sa in sauya ta ta fahimci muhimmanci ilimi. Zan fadakar da ita muhimmancin neman ilimi, amma kazama kuwa kazantarta za ta iya haifar mana da cututtuka har idan ba a yi sa’a ba ta kawo mutuwa.

Abincin da kazama za ta girka wa mutum ba ya da kwanciyar hankali ya ci, idan aka shigo gida komai a wargaje, kudaje sun cika ko’ina, ban daki ba a wanke ba, tana hamami, mutum ba zai iya kusantarta ba.

Miji zai rika jin kunyar ya kawo abokansa, domin ya san kunya zai sha saboda kazantar matarsa. Haka idan mutum ya haihu ma ’ya’yansa za su tashi da kazanta domin an ce da na gaba ake gane zurfin ruwa.

Dabi’ar kazanta ba kasafai ake iya sauya ta ba, domin na sha ganin mai ilimi ko kudi amma za ka gan ta kazama, amma idan ka auri jahila za ka sanya ta a makaranta komai dakikancinta sai ta hadu da dalibai ’yan uwanta sun koya mata wasu abubuwa.

Kazama zan zaba – Usman Danbaba

Daga Musa Kutama, Kalaba

Usman Danbaba: Ai da in zabi auren jahila gara kazama. Kazamar nake so, domin ita zan rika gaya mata tana gyarawa, a hankali zan gyara ta har ta zama mai tsabta. Ita kuwa jahila ai sai a hankali, komai nata a lalalce yake; jahilci bai yi ba a rayuwa.

Gara in auri kazami da in auri jahili – Hauwa Balarabe

Daga Ahmed Ali, Kafanchan

Hauwa Balarabe: A gaskiya da in auri miji jahili gara in auri kazami. Dalili shi ne, na farko idan na auri jahili wane irin zama za mu yi da shi? Shi ba ga ibada ba, ba kuma ga iya mu’amala ba. Malam Bahaushe yakan ce jahilci ya fi hauka. Shi jahili kullum yana ganin daidai yake yi koda ko yana tafka kuskure ne.

Kuma jahili zama da shi yana da matsaloli da yawa, misali zai bata kuma zai batar da iyalinsa  saboda ta san mijinta ne idan ta saba masa yana iya dukanta ma don bai san darajarta ba, yana iya zagin iyayenta, yana iya wulakanta ta da duk wani mai daraja a gare ta saboda jahilcinsa, kuma ba zai yarda ta yi masa gyara ba koda ya yi kuskure saboda jahilcinsa.

Idan an koma bangaren ibada da tarbiyya ma akwai gagarumar matsala. Ko ta ina fa jahilci bai yi ba sam-sam. Shi kuwa kazami na san idan na aure shi zan iya canja shi alal akalla koda ba duka ba, zan iya janyo hankalinsa da ayoyi da hadisai da kuma misalai a kan muhimmanci da amfanin tsabta, sannan zan rika yi masa wanki, in kai masa ruwan wanka in lallashe shi har sai ya yi wanka, sannan in lallabe shi har sai ya yi aski, kuma zan iya lallabarsa in rika yanke masa farcensa. Kuma zan rika yi masa kwatance da mutane masu tsabta har sai ya ji yana son tsabtar, kuma in na ga kaya masu kyau zan kwadaita masa ya saya, in ma ba ya da halin saye idan ina da shi zan saya masa, har sai na ga ya fito yadda nake so. Kuma zan yi kokari in hada shi abota da masu tsabta har ya kwadaitu da tsabtarsu, in sha Allahu.

Gara in auri kazama da na auri jahila – Kabir Abdullahi

Daga Ahmed Ali, Kafanchan

Kabir Abdullahi: A tawa fahimtar, gara in auri kazamar  mace a kan mace jahila. Dalilina shi ne, na farko dai mace kazama za ta iya ba ’ya’yanka tarbiyya sannan za ta zama mai sauki wajen yi maka biyayya, domin akasarin mata kazamai ba su da girman kai sosai; ka ga wannan dalilin ma kadai zai sa mutum ya samu sauki wajen canja matarsa daga halin kazanta zuwa na tsabta. Sabanin mace jahila wacce ba ta ma san ina ta fito ko ina za ta je ba, domin ka san an ce jahilci ya fi hauka wuyar magani; wanda ina ganin wannan karin maganar ma kadai ya ishi zama amsar tambayarka.

Mace ma tana da ilimi yaya aka kare da ita ballantana a ce ba ta da ilimin kwata-kwata? Ka ga ai ka daukar wa kanka gagarumin aiki. Kunyata ka da mace za ta yi da kazantarta a cikin gida bai kai kunyataka da za ta rika yi da jahilcinta a gida da waje ba, musamman a wannan zamanin da hanyoyin ilimanta suka yawaita, amma kuma duk da haka ta kasance mace jahila to ta ina ke nan za ka fara idan ka auro irin wannan mace?