✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wace ce mace?

Mace ta kasance tamkar wani furen fulawa, wanda idanuwan mutum suke sha’awar kallo a koyaushe, ita fulawa ta kasance abu mai kamshi. Haka  bayan kyawun…

Mace ta kasance tamkar wani furen fulawa, wanda idanuwan mutum suke sha’awar kallo a koyaushe, ita fulawa ta kasance abu mai kamshi. Haka  bayan kyawun kallo, tana bukatar kasancewa a cikin inuwa, domin idan aka sanya ta a rana za ta yi yaushi. To tamkar haka mace kan kasance wajen sanyaya zuciya da sanya farin ciki a zuciyar abokin rayuwarta.

Wannan kuma tun ran gini  tun ran zane, domin kuwa mace, tun tana karamar yarinya ta kasance mai kokarin son yin hidima ga wani, domin hatta wasanta na yarinta ba ya wuce na kula da jaririyarta (’yar bebi) ta kara ce,  ko ta  roba, tare kuma da son taya mahaifiyarta aikin gida.

Kuma a gaba haka za ta kasance har bayan ta girma ta yi aure inda take zama rumfa, kuma ta zama garkuwa ga dukan mutanen gida ta hanyar sadaukar da rayuwarta domin ta faranta musu da haskaka masu hanyar rayuwa. Wannan ya ta’allaka tun daga mijinta da ’ya’yanta da dangin mijinta da makwabtanta. Za ta kasance cikin hidimarsu ta yadda takan kasance tamkar wata baiwa wadda ita ba ta ma san wani abu jin dadi ba. Haka za ta rika gudanar da hidima ga iyalinta, kowa sai  ya riga ta kwanciya barci, kuma ta riga kowa tashi don ta share musu fagen fara rayuwa a wannan sabuwar rana.

Da  haka kuruciyarta  take tafiya cikin hidimar gyaran al’ummarta, wato da kyawunta da karfinta da komai nata a hankali za su gushe amma ba ta damu ba, matukar dai za ta sanya wa kowa farin cikin rayuwa da dora al’umma zuwa ga ingantacciyar rayuwa.

Duk a cikin wannan fadi-tashin da mace take yi, abin da kawai take  nema shi ne a nuna mata kauna da soyayya ta gaskiya ba tare da an ci amanarta ba ta kowace fuska.

Allah Sarki, mace ke nan, baiwar Allah. Sai dai hakan yana gagara daga  wajen mafi yawanmu maza. Yayin da wadansunmu suka dauke ta kawai tamkar abin biyan bukata, wacce ba ta da wani gata da daraja illa kawai ta biya wa mutane bukatunsu, ta gusar musu da sha’awarsu. Wannan ya yi kama da yadda aka dauki mace a zamanin Jahiliyya. Su kuma Turawan yanzu suka dauki mace a matsayin wacce za ta kure kyawun fuskarta, ta bude adonta da wasu bangarori na  sassan jikinta,  kawai domin jama’a su gani su yi dariya, su ji dadi, saboda haka suka mai da ita ’yar talla ko aikin banki, ko kuma ’yar aikin shaguna, ko ’yar fim. Ko mai watsa shirye-shirye a cikin tashoshin talabijin, ko ta watsa daddadar muryarta a cikin rediyo jama’a suna saurare, ko ma ta koma wacce za a saka hotunanta a cikin abubuwan sayarwa, ta rika kwaye tsiraicinta tana fitinar al’umma da kyawun surarta, tana sayen fushin Allah ga kanta da sauran mutanen duniya.

Su manufarsu kawai ita ce, domin ta janyo musu kasuwa ga abin da suke sayarwa, ita kuma ta nema wa kanta mummunan karshe tun a nan duniya.Kuma ta  hadu da azabar Allah a gobe Kiyama, ta kasance daga cikin makamashin wuta. Allah Ya tsare mu.

Addinin Musulunci tun farkon zuwansa ya karrama ta, ya ’yantar da ita, ya ba ta hakkinta tamkar namiji wajen samun sakamako a kan wahalhalunta tun a nan duniya.

Mata ku gode wa Allah a kan zuwan addinin Musulunci, kuma ku gode wa Allah, idan har Ya hallicce ku Musulmi, ku bi Allah, ku bi Sunnar AnnabinSa (SAW), ku yi koyi da iyayen muminai domin ku shimfida rayuwa ingantacciya. Kuma ku samar da ’ya’ya nagari, ku ba su tarbiyya tagari, a karshe su zama mutane nagari, a samu shugabbani nagari, ko ma’aikata nagari, ko ’yan kasuwa nagari, ko malamai nagari. Kun ga dalilinku sai a samu al’umma tagari. Allahu Akbar sanadin mace duniya duk ta zama tagari.

Mu kuma maza mu lura da yadda addininmu ya karamma mace, ya ba ta girma da daraja, wanda shi ne dalilin da ya sanya muka dauke ta da daraja. Mu yi nazarin rayuwar Annabawa (AS), da salihan bayin Allah, yadda suka yi zamantakewarsu da matansu suka yi hakuri da su suka faranta musu rayuwa, suka nuna musu soyayya ta gaskiya ta tsakani da Allah. Idan muka yi nazarin a kan wadannan abubuwan za mu sauke nauyin da Allah Ya dora mana a kan mata. Kuma idan aka tambaye mu a kan abubuwan kiwonmu wadanda mata suna cikinsu, to, a nan za mu bayar da amsa muna masu farin ciki da jin dadi.

Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce, “Dukkanku masu kiwo ne, kuma za a tambaye ku a kan abin da aka ba ku kiwo.”  Lallai magabatanmu sun yi adalci wajen nuna girman ’ya mace, kuma sun nuna matsayinta da sadaukarwarta.

A karshe, Allah Ya sa mu kasance masu riko da gaskiya ba son zuciya ba.

Za a iya samun Nata’ala a [email protected]