✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wadanda suka kamu da Coronavirus a Najeriya sun kai 81

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta ce an samu karin mutum 11 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya. Wannan…

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta ce an samu karin mutum 11 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya.

Wannan ya sa adadin mutanen da zuwa yanzu aka tabbatar sun kamu da cutar ya kai 81.

“Zuwa karfe 11:55 na daren ranar Juma’a 27 ga watan Maris, an tabbatar da karin mutum 11sun kamu da COVID-19”, a cewar sanarwar da hukumar ta NCDC ta wallafa a shafinta na Twitter.

An dai samu karin mutanen ne a Yankin Legas inda aka sanar da karin mutum takwas; sai kuma jihar Enugu inda aka samu mutum biyu da kuma mutum daya a jihar Edo.

A cikin mutum 81 har yanzu mutum daya ne ya rasa ransa sanadiyyar cutar yayin da aka sallami mutum uku tun bayan barkewar cutar a Najeriya.

A cewar hukumar NCDC  jihohin su ne:

Lagos- 52

Abuja- 14

Ogun- 3

Ekiti- 1

Oyo- 3

Edo- 2

Bauchi- 2

Osun-1

Rivers-1