Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta sanar da karin mutum biyar da suka kamu da cutar Coronavirus a kasar.
An samu karin mutane biyu a Yankin Babban Birnin Tarayya, da biyu a Legas, sai kuma guda a Jihar Ribas.
Hakan ya sa adadin mutanen da suka kamu da cutar a Najeriya ya kai 51.
A ranar Laraba kadai an samu karin mutane bakwai da suka kamu da cutar.
A yanzu haka an tabbatar da akwai masu dauke da cutar a jihohi kamar haka: mutum 32 a Jihar Legas, a Yankin Babban Birnin Tarayya akwai mutum 10, a Jihar Ogun mutum uku, sai kuma jihohin Ekiti daya, Oyo daya, Edo daya, Bauchi daya, Osun daya, da kuma Ribas daya.